@ Katsina times
Katafaren shagon nan mai suna AL -MUSIK VENTURES dake da wuri titin "yan kaji kasuwar Katsina da kuma Babban wurin shi dake bakin gadar kasa ta kofar kaura Katsina ya fara aiki gadan gadan awa 24.
Katsina times ta samu wata sanarwar da kantin ya bayar wanda aka dora a shafukan sada zumunta suna isar da sakon cewa yanzu suna kasuwancinsu a katafaren shagonsu na kofar kaura na tsawon awa 24.
Jaridun katsina times sun tabbatar da wannan sakon sanarwar, wanda suka bincika cewa komin dare, kazo zaka iya sayayya a kantin.
AL - MUSIK ya zama kantin farko da ya fara aiki awa 24 a mafi yawan jihohin kasar nan,wannan ya sanya ya zama zakaran gwajin dafi.
Bayan aiki awa 24 Al musik ya na da saukin kaya wanda ba Wanda ya kaishi a duk fadin jahar katsina. Kuma dukkanin kayan sa daga ingantatun kamfanoni wadanda suka shahara ake kawo su.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
07043777779