Gwamnatin Katsina Da UNICEF Sun Shirya Kaddamar Da Allurar Rigakafin Polio Da Masassarar Cizon Sauro

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24092025_095020_FB_IMG_1758706798382.jpg



Daga Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times 

Gwamnatin Jihar Katsina tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa a fannin kiwon lafiya sun ƙarfafa shirye-shirye na kaddamar da shirin rigakafin shan inna (polio) da masassarar cizon sauro (measles-rubella) a watan Oktoba 2025, wanda zai kare miliyoyin yara a fadin jihar.

A wajen taron tattaunawa da manema labarai da aka gudanar a Katsina Guest Inn a ranar 23 ga Satumba 2025, Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama R.M. Farah, ya jaddada muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen tabbatar da nasarar shirin.

“Muna son kowane yaro ya samu damar rigakafi. Wannan zai tabbata ne idan iyaye da al’umma sun fahimci muhimmanci da kuma tsaron wannan allura,” in ji Farah.

UNICEF ta bayyana cewa Jihar Katsina ta karɓi fiye da kashi 3.6 miliyan na sabuwar allurar rigakafin shan inna (nOPV2) wadda za ta kai ga yara miliyan 2.3 ‘yan ƙasa da shekaru biyar. Haka kuma yara miliyan 4.8 masu shekaru 9 zuwa 14 za a yi musu rigakafin masassarar cizon sauro (measles-rubella) tsakanin 4 zuwa 13 ga Oktoba 2025.

Akwai ƙungiyoyi 2,253 da za a tura, kowacce da mambobi 11, domin gudanar da aikin ta hanyar cibiyoyin dindindin da kuma ƙungiyoyin sintiri. Haka kuma an kafa ƙungiyoyi 200 na sasanta rashin amincewa da za su haɗa shugabannin gargajiya, Malaman Addini da masu rigakafin, domin shawo kan masu ƙin yarda da shirin.

Jihar Katsina za ta tura ƙungiyoyin lafiya 5,584, ciki har da ƙungiyoyi 3,761 masu zagayawa daga gida zuwa gida, da ƙungiyoyi 993 a hanyoyi da wuraren wucewa, da ƙungiyoyi 830 a cibiyoyin dindindin. UNICEF ta tallafa wajen horas da ma’aikatan lafiya fiye da 3,300 tare da masu sa ido 600 domin ƙara ƙwarewa da inganta hulɗa da al’umma.

Sakataren Hukumar Kula da Lafiyar a Matakin Farko ta jihar Katsina, Dakta Shamsuddeen Yahya, ya bayyana shirin da cewa “rigakafi ne na haɗa-hɗe,” inda za a yi polio tare da masassara da ake kira  (measles-rubella).

“A karo na farko, Katsina za ta gabatar da rigakafin rubella tare da masassara (measles-rubella). Wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci ganin tasirin cututtukan ga yara. Burinmu shi ne mu kai ga dukkan yara masu shekaru 9 watanni zuwa 14 a cikin kwanaki 10,” in ji Yahya.

Ya jaddada muhimmancin yaƙi da ƙarya da yaɗa jita-jita, yana tunawa da yadda yaɗuwar labaran karya lokacin COVID-19 da rigakafin HPV suka jawo ƙin amincewa. “Wannan taro da ‘yan jarida zai taimaka wajen yada sahihan bayanai da kuma gina amincewar iyaye,” in ji shi.

Shugabannin gargajiya da na addini, shugabannin kananan hukumomi da ‘yan majalisu sun riga sun sha alwashin goyon bayan shirin, ciki har da bayar da tsaro ga ƙungiyoyin rigakafi a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

Ko da yake UNICEF ta yaba da nasarar da aka samu wajen rage cutar polio daga rahoton mataki na 17 a shekarar 2024 zuwa na biyu a bana 2025, ta jaddada cewa har yanzu akwai buƙatar ƙarin ƙoƙari don kawo ƙarshen yaduwar cutar baki ɗaya.

Shirin rigakafin haɗin gwiwar nan zai gudana a dukkan kananan hukumomin Katsina, tare da haɗa kai da shirin ƙasa baki ɗaya na rigakafin yara.

Follow Us