Injiniya a Katsina Ya Kera Motar Sulke “Begua” Don Kare Al’umma

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26092025_142924_FB_IMG_1758896899480.jpg




Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

Wani ɗan asalin Katsina, Injiniya Ibrahim Lawal Dankaba, ya ƙera wata mota ta sulke ta zamani da ya radawa suna “Begua”. Kalmar “Begua” a Hausa tana nufin wata dabba (porcupine), mai kare kanta da ƙaya idan an takura mata.

A zantawa ta musamman da Katsina Times, Injiniya Dankaba ya bayyana cewa manufar ƙirƙirar wannan mota ita ce don taimakawa wajen kare al’umma da kuma cike gibi wajen tsaro.

“Begua ba don kai hari aka yi ta ba, amma idan aka kawo wa al’umma hari, za ta iya kare su kamar yadda dabbar take kare kanta,” in ji shi.

Motar sulken ta bambanta da yawancin irin ta, domin tana da taya masu “track” irin na APC maimakon na roba, abin da ya sa ta dace da hanyoyin da ke cikin dausayi, gona, ƙasar laka da ƙauyuka. Hakan zai ba ta damar motsi ba tare da ta makale ba, tare da kare mutanen da ke cikinta daga harbin bindiga.

Dankaba ya bayyana cewa aikin ya fara tun kusan shekaru biyu da suka wuce, a lokacin da hare-haren ‘yan bindiga da ta’addanci suka tsananta a Arewa. A halin yanzu an kai motar zuwa matakin gwaji na farko, inda ake shirin gudanar da nune-nunen gwaji a bainar jama’a da manema labarai.

Ya jaddada cewa wannan ƙirƙira ba ta maye gurbin jami’an tsaro ba, illa kawai don ƙarfafa su da kuma haɗa kai da al’umma wajen tsaron rayuka.

“Wannan aikin haɗin gwiwa ne. Muna son taimakawa gwamnati da jami’an tsaro, tare da ƙarfafa gwiwar al’umma cewa ana ɗaukar matakan da za su taimaka wajen tsaro,” in ji shi.

Katsina Times za ta kawo cikakken rahoto da bidiyo kan aikin Begua a tashoshinta, ciki har da Katsina Times TV (YouTube) da Katsina City News (Facebook).

Follow Us