Dangote Refinery Ta Karyata Rahotannin Sallamar Ma’aikata, Ta Ce Sauye-sauyen Tsaro da Tsarin Aiki Ne Kawai

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26092025_150735_FB_IMG_1758876456104.jpg


Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 26 ga Satumba, 2025

Matatar Mai ta Dangote da ke Lekki, Jihar Legas, ta yi karin haske kan labarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar nan game da zargin sallamar dukkan ma’aikata ’yan Najeriya.

A cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Juma’a, matatar ta ce ba a yi wannan sauyi don nuna wariya ga ma’aikata ba, illa dai tsari ne na sake fasalin ayyuka da tsaurara matakan tsaro sakamakon hare-haren barna da aka sha fuskanta a wasu sassan matatar.

“Wannan mataki ba na zalunci ba ne, an ɗauke shi ne domin kare rayukan ma’aikata, kiyaye kayayyakin kamfanin, da kuma tabbatar da dorewar ayyuka ga ’yan Najeriya da abokan hulɗa a duk fadin Afirka,” in ji sanarwar.

Kamfanin ya tabbatar da cewa fiye da ma’aikata 3,000 har yanzu suna ci gaba da aiki a matatar, inda kaɗan ne abin ya shafa. Haka kuma ya bayyana cewa ana ci gaba da ɗaukar sababbin ma’aikata ta hanyar shirye-shiryen horas da matasa masu digiri da shirin ɗaukar ƙwararru.

Dangote Refinery ta sake nanata aniyarta na bin ƙa’idojin ƙwadago na duniya, ciki har da ’yancin ma’aikata shiga ƙungiyoyin ƙwadago ko a’a. “Kare haƙƙin ma’aikata da mutunta su abu ne da ba mu taɓa kawar da kai daga gare shi ba,” in ji sanarwar.

Kamfanin ya ƙara da cewa manufar kafa matatar ita ce don bauta wa ’yan Najeriya, ƙarfafa dogaro da kai a fannin makamashi a Afirka, da samar da ayyukan yi masu dorewa.

A ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2025, wasu rahotanni sun bayyana cewa an sallami dukkan ma’aikatan Najeriya a matatar, bisa wata takarda da aka danganta da shugaban ma’aikata na kamfanin, Femi Adekunle. Takardar ta umarci ma’aikata su mika kayayyakin kamfani da ke hannunsu tare da karɓar takardun sallama, tana mai danganta matakin da “yawaitar rahotannin barna” a cikin masana’antar.

Matakin ya jawo caccaka daga ƙungiyoyin ƙwadago. Ƙungiyar PENGASSAN ta tabbatar da ganin wannan takarda amma ta ce ma’aikatan za a dawo da su. Haka kuma ƙungiyar NUPENG ta yi Allah wadai da abin da ta kira “rashin mutuntawa ma’aikatan Najeriya.”

Rahoton Sahara Reporters ya danganta wannan rikici da batun kafa ƙungiyar ƙwadago a cikin matatar, inda aka ce sallamar ta biyo bayan matakin shiga PENGASSAN da wasu ma’aikata suka yi.

Duk da wannan ce-ce-ku-ce, kamfanin Dangote ya ce abin da ke gudana a halin yanzu ba sallamar ma’aikata gaba ɗaya ba ne, sai dai sake tsari da tsaurara matakan tsaro don dorewar aiki da kare lafiyar ma’aikata.

Follow Us