Tinubu Ya Buƙaci Ƙarin Haɗin Kai Yayin Da Nijeriya Ke Cika Shekara 65 da Samun ’Yancin Kai

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes27092025_115858_FB_IMG_1758974148173.jpg



Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su zauna cikin haɗin kai da zaman lafiya domin cigaban ƙasa baki ɗaya.

Wata sanarwa da Dakta Suleiman Haruna, Daraktan Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, ya sanya wa hannu, ta ce Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, a lokacin sallar Juma’a ta musamman da aka shirya a matsayin wani ɓangare na bukukuwan cikar Nijeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai.

Shugaban Ƙasa, wanda Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya wakilta, ya bayyana cewa Nijeriya za ta iya cika mafarkin ubannin ƙasa ne kawai idan ’yan ƙasa sun zauna cikin zaman lafiya, sun jure bambance-bambancen su, kuma sun dage wajen aiki tuƙuru.

Ya ƙara da cewa ko da yake ƙasar nan tana cikin wani yanayi na sauyi, gwamnatin Tinubu tana samun cigaba a hankali wajen shawo kan matsalolin da ake fuskanta.

Ya yi kira ga ’yan ƙasa da su yi haƙuri yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin juya halin da tattalin arzikin ƙasa yake ciki.

Yayin da yake taya ’yan Nijeriya murnar cikar ƙasar nan shekara 65 da samun ’yancin kai, Shugaban ya roƙe su da su ci gaba da yin addu’a ga shugabanni da ƙasa domin samun makoma mai haske.

Dangane da taken bikin na bana, wato “Nijeriya a 65: A Haɗa Kai Don Gina Ƙasa Mafi Girma,” ministan ya ce Shugaban Ƙasa na kira ga ’yan Nijeriya gaba ɗaya, ba tare da la’akari da ƙabila, addini, bambancin siyasa ko matsayi ba, da su haɗa kai domin gina Nijeriya wadda muke mafarki da ita.

Ya kuma lissafa wasu nasarori da gwamnatin Tinubun ta samu, inda ya ce Nijeriya ta samu gagarumin cigaba a ɓangarorin tattalin arziki, tsaro, noma, da kuma wasu muhimman sassa.

Ya kuma yi wa al’ummar ƙasa fatan a yi bukin cikin zaman lafiya da murna.

Follow Us