Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA) ta gudanar da taron gangamin wayar da kan jama’a a kasuwar Charanci, Jihar Katsina, domin karfafa matasa da sauran ‘yan kasa masu cancanta su yi rajistar zabe.
An gudanar da taron ne a ranar Lahadi, 28 ga Satumba 2025, tare da halartar manyan baki da suka hada da Aminu Ishaq, sakataren karamar hukumar Charanci wanda ya wakilci shugaban karamar hukumar; wakilin Sarkin Shanu, Hakimin Charanci; da kuma shugaban kasuwar Charanci.
Daraktan hukumar NOA a Jihar Katsina, Mukhtar Lawal Tsagyam, ya yi kira ga matasa da sauran ‘yan kasa da ba su taba yin rajistar zabe ba da su gaggauta amfani da damar da ake da ita.
“Manufar wannan gangamin shi ne a karfafa matasa masu shekaru 18 ko sama da haka su fara rajista ta yanar gizo sannan su kammala a cibiyoyin INEC. Amma wajibi ne su tabbatar ba su taba yin rajista ba a baya. Wanda ya yi rajista fiye da daya zai iya rasa dukkan rajistarsa,” in ji Tsagyam.
Ya kara da cewa, duk wanda zai yi rajista dole ya kasance ya kai shekara 18, ya kasance ɗan Najeriya, kuma bai taba yin rajista ba a baya.
Tsagyam ya kuma yi bayani cewa wadanda suke da matsaloli a takardun katin zabe su garzaya ofisoshin INEC domin yin gyara maimakon sake yin sabuwar rajista. Wannan ya hada da wadanda suka rasa katin su, wadanda hoto ko rubutun katin ya lalace, wadanda ke son canza wurin kada kuri’a, da kuma wadanda sunayensu ko ranar haihuwarsu da aka yi kuskure a kan katin.
Hukumar NOA ta kuma yi amfani da wannan dama wajen tunatar da jama’a muhimmancin zama masu lura da tsaro. Tsagyam ya shawarci jama’a da su rika kai rahoton duk wani motsi ko wani abun shakka da basu gane ba, ga hukumomin tsaro maimakon daukar doka a hannu.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su yaba da ayyukan raya kasa da ake gudanarwa a Jihar Katsina daga gwamnatin jiha da ta tarayya.
“Muna iya ganin dimbin ayyukan da ake aiwatarwa daga gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Malam Dikko Umar Radda da kuma na gwamnatin tarayya a karkashin shugaban kasa. Ya kamata jama’a su yaba da irin wadannan kokarin,” in ji shi.
Yakin wayar da kan da aka gudanar a kasuwar Charanci wani bangare ne na shirin NOA na kasa baki daya domin karfafa halartar jama’a a harkokin siyasa da zabe mai zuwa.