Gwamna Radda Ya Naɗa Abdullaziz Mai Turaka A Matsayin Babban Mai Taimaka mashi Na Musamman Kan Wayar Da Kan Al'umma

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30092025_082519_FB_IMG_1759220654841.jpg


Katsina Times | 30 ga Satumba, 2025

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, ya amince da naɗin Abdullaziz Mamuda (Mai Turaka) a matsayin Babban Mai Taimakamasa na Musamman kan wayar da kan al'umma (Senior Special Assistant on Mobilization).

Wannan naɗi na cikin jerin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka don ƙarfafa haɗin kai da wayar da kan al’umma, tare da tabbatar da cewa manufofin gwamnatin Radda sun samu isarwa ga kowane yanki na jihar.

A cikin wasiƙar naɗin da Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Garba Faskari, ya sanya wa hannu, an bayyana cewa Mamuda ya samu wannan dama ne saboda sahihancin amincewar gwamnati cewa zai yi aikin da gaskiya, jajircewa, da kuma kishin jama’a.

“Wannan naɗi ya dogara ne da tabbacin cewa za ka yi aiki da amana da jajircewa a cikin al’umma, tare da tabbatar da cewa kana yin hidima a mafi kyawun maslaha ta jihar Katsina,” in ji Faskari a cikin wasiƙar.

Ya ƙara da cewa, “Ina taya ka murna bisa wannan naɗi, tare da yi maka fatan alheri da taimakon Allah don gudanar da wa’adin ka cikin nasara. Inji Faskari 

Babban Mai Taimakawa na Musamman kan wayar da kan jama'a (SSA on Mobilization) na ɗaya daga cikin muƙaman da ke da muhimmanci a tsarin mulkin gwamnatin jihohi. Mukamin na da alhakin haɗa kai tsakanin gwamnati da al’umma ta hanyar shirye-shirye na wayar da kan jama’a, ƙarfafa goyon bayan manufofin gwamnati, da kuma jagorantar tsarin faɗakarwa musamman a lokacin da ake aiwatar da manufofi masu tasiri.

Naɗin Abdullaziz Mamuda ya nuna aniyyar Gwamna Radda na ci gaba da dogaro da matasa masu ƙwarewa da jajircewa wajen jagoranci, domin ganin jihar Katsina ta samu ci gaba mai ɗorewa.

Wannan mataki na daga cikin dabarun gwamnatin Radda na samar da shugabanni masu hangen nesa da zasu iya jan hankalin jama’a wajen marawa manufofin gwamnati baya, musamman a fannin tattalin arziki, tsaro, da ilimi.

Follow Us