Cikar Jihar Katsina Shekaru 38: Ruwan Godiya Ya Gargadi ’Yan Jarida Kan Dogaro da Gwamnati

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02102025_093339_FB_IMG_1759395959495.jpg

Katsina Times 

Wani masani a fannin yada labarai kuma malami a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usman Katsina, Malam Bashir Usman Ruwan Godiya, ya gargadi ’yan jarida da su daina dogaro da abin da gwamnati ke bayarwa a matsayin tallafi, domin hakan na rage darajar aikin jarida tare da raunana dimokuraɗiyya.

Ruwan Godiya ya bayyana haka ne a wani taron karawa juna sani na yini guda da Majalisar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Katsina ta shirya, mai taken: “Dimokuraɗiyya da Jaridancin Cigaba: Darasi daga Arewacin Najeriya.”

A cewar shi, ya zama wajibi ga ’yan jarida su guji zama muryar gwamnati kawai.

“Aikin jarida ba zai rayu ta hanyar kallon abinda gwamnati ta bayar ba. Idan ’yan jarida suka rungumi manhajar takardun manema labarai, alawus da kuma jakar kudi (brown envelopes), suna rasa ’yanci, gaskiya da amincewar jama’a,” in ji shi.

Ya ce irin wannan dogaro ya sa yawancin gidajen jarida a Najeriya sun fi maida hankali kan manyan ’yan siyasa, tare da barin muradun talakawa.

“Muna ta ruwaito jawaban shugabanni amma ba mu ba da dama ga muryar jama’a. Aikin jarida ya kamata ya koma kan nauyin dimokuraɗiyya,” in ji shi.

Malamin ya bayyana wannan hali a matsayin “jaridar kasuwanci” wacce ke mai da wasu ’yan jarida kamar muryar masu mulki kawai. Ya ƙalubalanci ’yan jarida da su rungumi jaridar bincike, ta nazari da kuma ta jama’a, maimakon jiran sadaka daga gwamnati.

Ya ƙara da cewa “Sadakar gwamnati ba za ta iya ciyar da jarida ba har abada. ’Yanci, bincike da ƙwarewa su ne kadai hanyoyin da za su dawo da martaba da kare dimokuraɗiyya.”

Haka kuma, Ruwan Godiya ya nuna ƙarancin horo, son zuciyar masu gidajen jarida da kuma rashin walwala ga ma’aikata a matsayin ƙalubale da ke addabar aikin jarida. Amma ya jaddada cewa matakin farko shi ne ’yan jarida su kubuta daga dogaro da gwamnati domin samun jarida mai ƙarfi da kuma ’yanci.

Follow Us