Katsina Times, 2 Oktoba, 2025
Gwamnatin Jihar Katsina ta gudanar da babban taron wayar da kai da horarwa domin ƙarfafa gaskiya, bin doka da oda, da kuma sa ido kan aiwatar da manufofin gwamnati a matakin ƙananan hukumomi, wanda ya haɗa kansiloli 361 daga gundumomin jihar.
Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Katsina ce ta shirya taron, inda Gwamna Dikko Umar Radda, PhD, ya jagoranci kaddamar da taron a dandalin Hukumar Kula da Ƙananan Hukumomi da ke Katsina a ranar Alhamis.
Gwamna Radda ya bayyana shirin a matsayin “mataki mai matuƙar muhimmanci wajen gina gaskiya daga tushe,” inda ya jaddada wa kansiloli muhimmancin rawar da suke takawa wajen kare dukiyar jama’a.
“Wannan shiri ba wai kawai game da yaƙi da rashawa ba ne, ya shafi kare al’ummarmu, albarkatunmu da kuma makomar ’ya’yanmu,” in ji shi.
An tsara horon ne domin bai wa kansiloli dabarun gudanar da ingantaccen bincike kan ayyukan gwamnati, tabbatar da bin doka da oda, da kuma hana ɓarnar kuɗaɗe a matakin ƙananan hukumomi.”
Mai ba da shawara na musamman kan harkokin ƙananan hukumomi, Lawal Rufa’i Safana, ya jaddada cewa kansiloli su rungumi rawar da doka ta ba su wajen kare gaskiya.
“Duk wanda yake bin doka kuma yake da ikon kula da aiwatar da ita, lallai ana sa ran shi ne zai hana rashawa. Wannan shi ne dalilin da yasa kuke zama sojojin ƙafa na wannan yaƙin da cin hanci,” in ji Safana.
Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci, Mai Shari’a Lawal Garba, (Ritaya) ya yi gargaɗi cewa cin hanci na bunƙasa idan aka yi shiru, inda ya bayyana kansiloli a matsayin “zuciyar dimokuraɗiyya a matakin ƙasa.”
“Duk wata kwangila da aka ƙarama kuɗi abinci ne aka kwace daga bakin wasu iyali. Kowa wane aiki da aka ƙi aka barshi a tsakiyar hanya, al’umma ce aka hana hakkinta. Kansiloli dole su tashi tsaye su yi magana,” in ji shi.
Garba ya kuma yaba da shirin Community Development Programme (CDP) na Gwamna Radda wanda ke ƙarfafa shiga al’umma cikin harkokin gwamnati, da Hukumar Katsina State Development Management Board wadda ke tabbatar da adalci da tsari wajen tsara ci gaban jihar.
Taron ya samu halartar fitattun jami’ai da dama, ciki har da Abdullahi Haruna Eka, shugaban kungiyar Kansiloli ta Katsina; Sha’aibu Aliyu, mai duba asusun jihar; Injiniya Abdularahman Kandarawa na majalisar dokoki; Dr. Umar Musa Yandaki; da Isyaku Mani Dandagoro. Da suka gabatar da lecture a wajen taron.
Sauran sun haɗa da Alhaji Rabo Tambaya Danja, mukaddashin shugaban ALGON a Katsina, da kuma Dr. Jamilu Lawal Charanci, darakta janar na hukumar cin hanci da karbar korafe-korafe.