Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina, ta sanar da dakatar da yajin aikin da ta shirya farawa a ranar Litinin, 6 ga Oktoba, 2025, bayan cimma wasu muhimman matsayai da Gwamnatin Jihar Katsina.
A cikin sanarwar da shugaban kungiyar, Dr. Murtala Abdullahi Kwarah, ya fitar a ranar Talata, 7 ga Oktoba, 2025, ASUU ta bayyana cewa tattaunawar da aka gudanar da shugabannin jami’ar da kuma masu ruwa da tsaki ta haifar da yarjejeniyoyi masu tsari a fannoni daban-daban.
1. Mallakar Portal ɗin Jami’a:
An amince da kafa kwamitin haɗin gwiwa wanda zai kunshi wakilan gwamnati da na ASUU domin bincikar batun mika portal ɗin jami’ar ga masu zaman kansu. Har zuwa kammala binciken, an dakatar da duk wani shirin mika portal ɗin.
2. Asusun Gwamnati Na Bai-daya (TSA):
Gwamnatin jihar ta amince da duba tsarin TSA da ake amfani da shi a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua domin daidaita shi da bukatun jami’ar, bisa doka da ka’idojin da suka kafa jami’ar da kuma hukuncin kotu.
3. Tsarin Inshorar Lafiya (KTSCHMA):
An gudanar da taro tsakanin ASUU da hukumar KTSCHMA inda bangarorin biyu suka amince da matsalolin da ke akwai, tare da kudurin ci gaba da tattaunawa har sai an cimma daidaito.
4. Tsarin Fensho:
Ba a samu cikakken ci gaba ba saboda rashin shugaban hukumar fansho, amma an tabbatar da cewa za a sake zama da zarar ya dawo domin duba bukatun ASUU.
5. Jadawalin Albashi da Sharuddan Aiki:
Duk da cewa ikon yanke hukunci yana hannun Gwamna (a matsayinsa na Visitor), an amince da sake rubuta wasika zuwa ga Gwamnatin jiha domin neman duba da amincewa.
Kungiyar ta bayyana cewa ta dakatar da yajin aikin har zuwa karshen watan Oktoba 2025, inda ake sa ran gwamnati za ta cika alkawuran da aka dauka.
Haka kuma, kungiyar ta jaddada cewa tana sa ran ganin an aiwatar da gyare-gyare kan jadawalin albashi da tsarin fansho kafin ƙarshen watan Oktoba.
ASUU ta kuma yi kira ga Gwamnatin Katsina da ta hanzarta warware matsalolin da suka shafi KTSCHMA da portal ɗin jami’a, domin guje wa jinkirin da zai iya shafar harkokin karatu.
Kungiyar ta mika godiya ga duk masu ruwa da tsaki da suka taka rawa wajen cimma daidaito, ciki har da Hukumar Gudanarwar Jami’a, Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, da sauran masu kishin ci gaban jami’a.
Sai dai ASUU ta yi gargadin cewa idan gwamnati ta kasa cika alkawuran da aka dauka kafin ƙarshen watan Oktoba, za ta dauki matakin da ya dace domin kare muradunta da walwalar mambobinta.
“ASUU-UMYU za ta ci gaba da kare ’yancin kai na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da walwalar mambobinta, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba idan aka sake yin watsi da bukatunmu,” in ji Dr. Murtala Abdullahi Kwarah, shugaban kungiyar.