MATSAYAR KUNGIYAR MA'AIKATAN JAMI'A WADANDA BASA SHIGA AJI (NASU) RESHEN JAMI'AR UMARU MUSA YAR'ADUA TA KATSINA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes07102025_153155_UMYU-Katsina.jpg

Kungiyar Ma'aikatan da basa shiga Aji (NASU) reshen Jami'ar Ummaru Musa Yar'adua, Katsina ta dauki tsawon lokaci tana bin masu ruwa da tsaki akan harkokin Jami'ar ta hanyar tuntuba da kai takardun korafe-korafe wadanda suka shafi mambobin ta da kuma ziyara ta tattaunawa da wasu daga cikin mahukunta da suka hada da Shugaban zartarwa Jami'ar, Shugaban Ma'aikata na Jaha, Kwamishina mai kula da harkokin Ilimi mai zurfi, shugabannin gudanarwar Jami'ar da sauransu, wanda haka bai haifar da wata mafita ba.

Duba da hakan, Kungiyar ta yanke shawarar tsunduma yajin aiki na gargadi na sati biyu a ranar Litinin 6/10/2025, tare da sauran Kungiyoyin Ma'aikatan Jami'ar guda 3 da suka hada da ASUU, SSANU da NAAT karkashin gamayyar hada ka ta In-house Unions. Sai dai biyo bayan wannan sanarwa yasa masu ruwa da tsaki akan harkokin Jami'ar suka gayyaci Kungiyar ta NASU tare da sauran Kungiyoyin guda 3 domin tattaunawa. 

Zama ya gudana tsawon wuni ukku inda aka zauna Ranar Alhamis, Juma'a da Kuma Lahadi (2nd, 3rd&5th October, 2025) inda aka tattauna da manyan masu ruwa da tsaki na Jami'ar da shugabanci Kungiyar na NASU kuma akasamu cimma yarjejeniyoyi kamar haka: 

1. Rikicin mamaye dandalin yanar gizo (portal) na Jami’a
An amince da kafa kwamitin hadin gwiwa wanda zai ƙunshi dukkan masu ruwa da tsaki tare da wakilan ƙungiya domin bincikar lamarin ta fuskar fasaha (technical) da doka (legal).
Saboda haka, an dakatar da mamayar dandalin har sai kwamitin ya kammala aikinsa ya fayyace halascin amfani da darajar wannan tsoma baki.

2. Asusun Gwamnati Na Bai-daya (TSA)
Gwamnati ta amince ta duba da gyara tsarin TSA da ake amfani da shi a UMYU domin dacewa da bukatun musamman na jami’ar. Wannan ya ta’allaka ne da ’yancin kai na jami’ar kamar yadda doka ta tanada a Miscellaneous Act, da dokokin kafa jami’ar, da kuma hukuncin Kotun Koli a kan haka.

3. Tsarin Inshorar Lafiya (KTSCHMA)
An gudanar da Zamabtare da shugabannin tsarin inshorar Lafiya ta Jaha inda suka amince da korafe-korafen da aka gabatar kuma suka yarda da matsalolin da ake fuskanta. Bangarorin biyu sun amince da ci gaba da tattaunawa har sai an warware dukkan matsalolin da gamsuwa.

4. Matsalolin Tsarin Fensho
Ba a samu tattaunawa ba saboda rashin Shugaban Hukumar ta Fensho, amma an tabbatar da cewa da zarar ya dawo za a kira taro domin duba bukatun da ƙungiya ta gabatar.

5. Teburin Albashi na Ƙasa da Yanayin Aiki (National Salaries, Incomes and Wages Commission Table)
Ba a kai ga wata  matsayaba ta zahiri ba ayayin zaman domin ikon amincewa da teburi na hannun Mai Ziyarar Jami’ar (Visitor) duk da hakan an amince da sake mika bukata a hukumance ga Gwamnatin Jihar domin duba ta da amincewa.

Matsayar Kungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'ar Wanda Basa Shiga Aji (NASU–UMYU)

Dangane da wadannan Fahimtocin da kuma amsar da wasu masu ruwa da tsaki suka bayar tare da damuwarmu game da ci gaban dalibai da sauran al'ummar Jami'ar, ƙungiya ta yanke shawara kamar haka:

1. Dakatar da yajin aikin da ta shirya farawa a Litinin, 6 ga watan Oktoba, 2025.
Wannan dakatarwa za ta yi aiki har zuwa ƙarshen watan Oktoba 2025, inda ake sa ran gwamnati zatayi abinda ake bukata.

2. Dangane da teburin albashi da zaɓin Kanfanin da zai kula da fansho, ana sa ran aiwatarwa kafin ƙarshen watan Oktoba, 2025.

3. Game da KTSCHMA da mamayar dandalin jami’a, bangaren  gwamnatin ta nuna cikakkiyar niyyar gyara da aiwatar da waɗannan bukatu.

4. Idan aka gaza magance matsalolin nan zuwa Karshen watan Oktoba, 2025, ƙungiyar za ta ɗauki matakin daya dace domin kare muradunta da na mambobin ta.

Muna mika godiya ga dukkan bangarorin da suka shiga tsakani wajen ganin an samu tattaunawa a wannan mawuyacin lokaci. Haka kuma muna godiya ga jama’a, kungiyoyin farar hula, manema labarai, iyaye, dalibai, tsoffin dalibai (alumni) da sauran ‘yan kasa masu kishin ci gaban jami’ar da kare haƙƙin mambobinmu.

NASU–UMYU za ta ci gaba da kare walwalar mambobinta, ’yancin kai da mutuncin Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, kuma ba za ta yi shakka ba wajen ɗaukar matakin dayadace ba idan ba a magance waɗannan matsaloli ba.

Ibrahim Amadu 
Shugaba, NASU - UMYU

Follow Us