Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya mika ragamar jagorancin hukumar ga Hajiya May Agbamuche-Mbu, wacce yanzu ta zama shugabar riko ta INEC.
Wannan sauyi ya kasance ne bayan kammala wani muhimmin taro da aka gudanar da Kwamishinonin Zabe na Jihohi (RECs) a hedkwatar hukumar da ke Abuja a ranar Talata, 7 ga Oktoba, 2025.
A lokacin da yake jawabi, Farfesa Yakubu ya tabbatar da cewa Agbamuche-Mbu ce tsohuwar kwamishiniya mafi dadewa a hukumar, don haka ya mika mata ragamar shugabanci har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban hukumar ta dindindin.
Ya kuma roki kwamishinonin jihohi da daraktocin INEC da su ba da cikakken hadin kai gare ta domin tabbatar da dorewar ayyukan hukumar. “Na roki dukkanmu da mu ci gaba da aiki tare da ita cikin gaskiya da kwarewa, har zuwa lokacin da sabon shugaban hukumar zai hau gado,” in ji shi.
Hajiya May Agbamuche-Mbu dai ta shahara wajen gudanar da manyan ayyukan zabe a Najeriya tun bayan nadinta a matsayin kwamishiniyar kasa a hukumar INEC.
Tuni dai wannan sauyi ya jawo cece-kuce a fagen siyasa, yayin da ake sa ran gwamnatin tarayya za ta sanar da sabon shugaban hukumar nan ba da jimawa ba.
Wannan sauyin jagoranci ya zo ne a daidai lokacin da hukumar ke ci gaba da gudanar da shirye-shirye na sake duba tsarin zabe da aiwatar da wasu daga cikin shawarwarin da wakilan Tarayyar Turai (EU) suka bayar bayan zaben 2023.
Ana sa ran Hajiya Agbamuche za ta ci gaba da gudanar da ayyukan hukumar kamar yadda doka ta tanada har zuwa lokacin da sabon shugaban zabe zai hau mulki na dindindin.