Daga Rahoton daily trust
@ katsina times
Jaridar daily trust ta yau laraba ta ruwaito cewa fulani dauke da makamai sun kai hari kauyuka da yawa a karamar hukumar kankia ta jahar katsina.
Jaridar tace harin ya faru ne a daren ranar litinin data gabata a garuruwan kwadawa dake Gachi da Bogga,Taiba Badole ,Arahiya kwadawa,Rumawa,Sugar Bindo fakuwa/ kahin dangi.
Jaridar tace Maharan sun kai su dari a bisa babura.
Jaridar tace, mazauna yankin kankia da kusada sun lura cewa tun bayan zaman lafiya da akace anyi a yankin funtua ake ganin fuskokin wasu bakin fulani a yankin.
Jaridar tace rundunar yan sanda sun tabbatar da harin kuma suna daukar mataki akai,