Katsina Times
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da sabbin jami’ai 200 na rundunar Community Watch Corps (C-Watch), wanda hakan ya kara fadada aikin tsaron al’umma zuwa kananan hukumomi 20 daga cikin 34 da ke fadin jihar.
An gudanar da bikin yaye jami'an ne a ranar Laraba, inda Gwamna Radda ya bayyana cewa shirin C-Watch wani ingantaccen tsari ne na cikin gida da gwamnatinsa ta kirkiro don dakile matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar Katsina.
“Lokacin da muka kaddamar da rundunar C-Watch sama da shekaru biyu da suka gabata, a cikin sabon mataki ne na gwaji. Abin da na tabbatar da shi kawai shi ne kudirin gwamnati na kawo karshen ta’addanci da ‘yan bindiga a Katsina. Na yi yakin neman zabe a kan hakan, kuma ba zan ci amanar jama’a ba,” in ji Gwamna Radda.
Sabbin jami’ai 200 da aka horas za a tura su zuwa kananan hukumomin Kankia da Dutsin-Ma. Dutsin-Ma na da iyaka da Safana, Danmusa da Matazu – wuraren da ke cikin jerin mafi yawan hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
Gwamna Radda ya karyata jita-jitar da ke cewa gwamnatinsa na tattaunawa da ‘yan bindiga, yana mai cewa gwamnatinsa ba ta shiga wata tattaunawa kai tsaye da su, sai dai tana marawa al’umma baya idan sun fara sulhu da wadanda suka tuba.
“Tsarin ‘Katsina Model’ na tsaron al’umma ne. Mutanen yankuna ne suke jagorantar tattaunawa da ‘yan bindigar da suka ajiye makamai, gwamnati kuma tana goyon bayan tsarin tare da tabbatar da doka da oda,” in ji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa shirin ya fara haifar da sakamako mai kyau, inda ya ce a Jibia ba a samu babban hari ba tsawon watanni takwas, sannan Batsari ta kwashe watanni bakwai cikin zaman lafiya. Haka nan an samu saukin matsalar tsaro a Danmusa, Safana, Faskari da Sabuwa.
Radda ya kara jaddada cewa gwamnatin jiharsa za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da jami’an tsaron tarayya, inda ya gargadi masu niyyar komawa aikata laifi cewa za su fuskanci hukuncin doka.
Ya kuma yaba da hadin kan da ke tsakanin gwamnatin jihar da rundunonin soja, rundunar saman Najeriya, da ‘yan sanda, wanda ya ce ya inganta bayanan leken asiri da gaggawar daukar mataki a lokutan kai hare-hare.
A nasa jawabin, Kwamishinan Tsaro Na Cikin Gida da Harkokin Gida, Dokta Nasir Mu’azu, ya ce Gwamna Radda ya rage matsalar rashin tsaro a jihar ta hanyar amfani da tsarin tsaro na al’umma.
“Wannan shi ne zagaye na uku na horar da jami’an C-Watch, bayan na farko a watan Oktoba 2023, da na biyu a watan Nuwamba 2024. Matasa ne da aka fito da su daga al’ummominsu, aka tantance su, aka horas da su domin kare iyayensu da ‘yan uwansu,” in ji Dokta Nasir.
Shugaban Kwamitin Rundunar C-Watch, Manjo Janar Junaidu Bindawa (Rtd), ya bayyana cewa jami’an sun samu horo mai zurfi kan dabarun yaki, kula da makamai, leken asiri da kuma yadda ake gudanar da tsaron al’umma.
“Ba a horas da su don su kawo matsala ba, an horas da su don su magance ta,” in ji Bindawa, yana mai jan hankalin jami’an da su yi aiki cikin ladabi da da’a tare da sauran hukumomin tsaro.
Ya kuma tuna cewa rundunar C-Watch tana karkashin doka ta musamman wacce Gwamna Radda ya rattaba hannu a kai a ranar 6 ga Satumba, 2023.
Janar Bindawa ya bayyana cewa nasarar Katsina ta jawo hankalin wasu jihohi, inda aka gayyace su don taimakawa wajen horar da irin wannan runduna a Zamfara da Kano.
Bikin ya samu halartar Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Hon. Abduljalal Haruna, wanda ya wakilci Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura. Haka kuma, shugabannin hukumomin tsaro, shugabannin kananan hukumomi, sarakuna da limamai da manyan jami’an gwamnati sun halarta.
Gwamna Radda ya yi kira ga sabbin jami’an da su yi aikinsu cikin gaskiya, mutunci da bin ka’idojin kare hakkin bil’adama.
“An dora muku nauyi ba kawai na tsaro ba, har ma na kare mutuncin Katsina da tabbatar da zaman lafiya da ci gaban al’umma,” in ji shi.
Shirin C-Watch na Gwamna Radda yana kara samun karbuwa a matsayin hanya ta tsaro ta al’umma da ke mayar da hankali kan haɗin kai, bayanan cikin gida da gina amincewa wanda ya sanya Katsina ta zama abin koyi ga sauran jihohin arewacin Najeriya.