An Fara Taron Horaswa Kan Kudin Intanet “Crypto” a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes25102025_182619_IMG-20251025-WA0192.jpg

Daga Muhammad Ali Hafizy, Katsina – 25 Oktoba, 2025

An shiga rana ta farko ta taron bayar da horo ga matasa kan harkar kudin intanet da ake kira “Crypto”, wanda cibiyar koyar da sana’o’i ta Katsina Vocational Training Center (KVC) ta shirya tare da hadin gwiwar Paracha Family daga Abuja.

Taron wanda aka fara gudanarwa a ranar Asabar, 25 ga Oktoba, 2025, yana da nufin fadakar da matasa game da yadda ake amfani da kudin intanet da kuma hanyoyin da za su kare kansu daga asarar da ke tattare da harkar.

A wajen taron, Malam Danjuma Katsina, wanda ke kula da cibiyar KVC, ya gabatar da jawabi inda ya bayyana tarihin kafuwar cibiyar da irin gudunmawar da take bayarwa wajen koyar da matasa sana’o’in dogaro da kai.

Ya kuma tunatar da mahalarta taron su maida hankali domin su amfana da abin da ake koyarwa, tare da yi masu alkawarin cewa bayan kammala horon, za a tura sunayensu zuwa hukumar KASEDA domin samun tallafi wajen ci gaban sana’o’insu.

Shi kuma Malam Abubakar Gwani Salisu daga jihar Kano, wanda shi ne ya jagoranci horon, ya bayyana ma mahalarta yadda sana’ar Crypto take, ribar da ke cikinta, da kuma matakan da ake dauka domin guje wa asara a harkar.

Taron na ci gaba da gudana, inda ake sa ran kammala shi a ranar Lahadi, 26 ga Oktoba, 2025.

Follow Us