Kwamishinan Tarayya Mai Wakiltar Jihar Katsina a Hukumar Gidaya ta Kasa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28102025_144623_Screenshot_20251028-154155.jpg


Kwamishinan Tarayya a Hukumar Kidaya ta Ƙasa (NPC), mai wakiltar Jihar Katsina, Injiniya Alhaji Bala Almu Banye, (Zarman Katsina) ya kammala wa’adin aikinsa na biyu bayan da ya shafe shekara goma yana gudanar da aikin hukumar.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 28 ga Oktoba, 2025, jim kadan bayan kammala taron bankwana da jami'an hukumar, tsohon kwamishinan ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa ga damar da ya samu na hidimtawa ƙasarsa cikin koshin lafiya da sakewa.

“Ina gode wa Allah da ya ba ni damar taka rawa a hukumar Kidaya ta Ƙasa a tsawon shekara goma. Na yi iya ƙoƙarina wajen tabbatar da cewa Jihar Katsina ta ci gajiyar wannan aiki da kasa baki daya.” in ji shi.

Injiniya Banye ya kuma gode wa Gwamnatin Jihar Katsina karkashin shugabancin Malam Dikko Umar Radda al'ummar jihar baki ɗaya bisa goyon bayan da suka ba shi, wanda ya ce hakan ne ya ba shi damar taka muhimmiyar rawa wajen wasu nasarorin da aka samu a lokacin aikin nasa.

Ya kuma mika godiya ta musamman ga Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, da tsoffin gwamnonin jihar; Rt. Hon. Aminu Bello Masari da Barrister Ibrahim Shehu Shema, bisa jagoranci da goyon baya tun daga shekarar 2014 zuwa yau.

Haka kuma, tsohon kwamishinan ya yi godiya ga Mai Martaba Sarkin Kasar Katsina, Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman, da Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji (Dr.) Umar Faruk Umar, bisa kulawa da goyon baya da suka nuna masa a tsawon lokacin da ya shafe yana shugabanci a hukumar.

Har wayau, a yayin da yake bankwana da ma’aikatan hukumar, Inkiniya Banye ya yaba da haɗin kan da ya samu daga jami’an hukumar, musamman daraktoci da ma’aikatanta a bangarori daban-daban.

“Na gode da yadda kuka ba ni haɗin kai. Ko da zan bar wannan ofishi, ina roƙonku da kowa ya saki jinkinsa, ku ci gaba da aiki da natsuwa, kar ku damu da barina. Doka ce ta tsara barin ofis bayan cikar wa’adi na biyu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa duk da cewa ba a gudanar da kidaya ba a cikin wa’adinsa, amma cikin ikon Allah an cimma muhimman abubuwa da suka tabbatar da shirye-shiryen da hukumar ke yi domin kidayar ƙasa nan gaba kadan.

“Mun kafa tubalin da za a iya ginawa a kai. Muna fatan wanda zai biyo baya, in ya zo, shi kuma ya dasa bisa abin da muka yi; ya zo ma ya zarce abin da muka yi. a. Wannan shi ne ci gaba!,” in ji shi.

Taron bankwanan ya samu halartar manyan jami’an hukumar, ciki har da Umar Sa’idu Waziri, Daraktan Hukumar a Katsina; Ado Mamman, HOD Civil Registration; Jamila Lawal Jibia, Jibia LGA Controller; Ibrahim Garba, HOD Technical; Zahara’u Mudi Kurfi, HOD Administration; da Ahmad Yakub, HOD Accounting, da sauran ma’aikata.

A ƙarshe, ma’aikatan hukumar sun karrama shi da kyautukan girmamawa da kuma shaidar karrama, tare da yi masa addu’ar fatan alheri a sabbin al’amuransa na gaba.

Follow Us