Save The Children Ta Kai Ziyarar Musamman Ga Gwamnatin Jihar Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes28102025_162757_FB_IMG_1761668833922.jpg



Daga Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times
 Talata, 28 Oktoba, 2025

Gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda ta karɓi bakuncin shugabannin ƙungiyar agaji ta Save The Children a matakin ƙasa Mr. Duncan Haver, yayin wata ziyara ta musamman da suka kai wa gwamnatin a ranar Talata, 28 ga watan Oktoba, 2025.

Tawagar ta samu tarba daga Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, wanda ya wakilci Gwamnan a lokacin ganawar da aka gudanar a Katsina.

Shugaban tawagar Save The Children Mr. Duncan ya bayyana cewa manufar ziyarar ita ce ganawa da gwamnatin jihar domin tattauna batutuwan da suka shafi lafiyar yara da iliminsu, tare da bayyana irin ci gaban ayyukan da ƙungiyar ke gudanarwa a sassan jihar.

Ya ce, “Mun zo ne domin tattaunawa da gwamnatin jihar Katsina kan yadda muke gudanar da ayyukanmu da kuma matsalolin da muke fuskanta, musamman a fannin kula da yara ƙanana masu fama da rashin lafiya sakamakon rashin abinci mai gina jiki. Wannan shi ne babban abin da ƙungiyarmu ta sa a gaba – taimakon rayuwar yara masu rauni.”

Duncan ya ƙara da cewa Save The Children na aiki a kananan hukumomi uku na jihar – Mashi, Kurfi, da Musawa – sakamakon yawan yara da ke fuskantar matsalar rashin zuwa makaranta a yankunan.

“Haka kuma, a duk lokacin da aka samu matsalar gaggawa kamar barkewar cutar kwalara ko wasu bala’o’i, ƙungiyarmu kan isa yankunan domin tallafa wa al’umma,” in ji shi.

A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Alhaji Abdullahi Garba Faskari, ya yi jinjina ta musamman ga ƙungiyar Save The Children bisa irin gudunmawar da take bayarwa wajen tallafawa yara da iyalai a fadin jihar.

Ya tabbatar wa tawagar cewa gwamnatin jihar tana kan shirin kafa kwamitin musamman da zai duba matsalolin da ƙungiyar ta gabatar, tare da neman hanyoyin da za su taimaka wajen magance su nan gaba kadan.

Faskari ya kuma tabbatar wa ƙungiyar da cikakken goyon bayan gwamnatin Katsina wajen ganin an cimma burin da ake nema na tabbatar da yara sun samu abinci mai gina jiki da ingantacciyar lafiya a fadin jihar.

Ziyarar ta ƙara nuna haɗin kai tsakanin gwamnatin Katsina da ƙungiyoyin agaji wajen inganta rayuwar yara da lafiyar jama’a baki ɗaya.

Follow Us