Rikicin Masallaci a Taraba: Rayuka Biyu Sun Salwanta — Ba Fada Bace Tsakanin Izala da Dariqa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30102025_094403_FB_IMG_1761817355189.jpg



Daga Abbas Usman, Jihar Taraba

An tabbatar da mutuwar mutane biyu da jikkatar wasu uku a rikicin da ya auku a Masallacin JIBWIS (Izala NHQ Jos) da ke garin Donga, Jihar Taraba, bayan takaddama ta kunno kai kan mallakar masallacin.

Rahotanni sun bayyana cewa masallacin, wanda kungiyar Izala ta mallake tun a shekarun 1980s, an sake gyarawa kwanan nan ta hannun wani amininsa na sarkin Donga. Bayan an kammala aikin, amininsa ya kira limamin masallacin domin ya mika masa makullin, amma sarkin ya ce ba zai mika wa ‘yan Izala na Jos ba, sai dai ‘yan dariqa. Sai dai ‘yan dariqa suka ki karɓa suna cewa masallacin na Izala ne.

An ce sarkin ya tuntubi wasu ‘yan Izala na Kaduna da Abuja don mikawa masallacin, amma su ma suka ce ba nasu bane, domin mallakar Izala NHQ Jos ne.

Takaddamar ta kai kotu, daga bisani aka nemi sulhu a cikin gida. Bayan janye karar daga kotu, sarkin ya sanya sharadin cewa dole a sauya limamin masallacin saboda yana daga cikin danginsu, yana zagin wasu. An amince da hakan domin zaman lafiya, amma daga baya sarkin ya nemi a nada sabon limami daga cikin ‘yan dariqa — abin da ‘yan Izala suka ki amincewa da shi, suna cewa masallacin ba na dariqa ba ne.

A daren da ‘yan Izala suka shirya bude masallacin don yin sallah washegari, wasu da ake zargin ba Musulmai ba ne suka kai musu hari, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya tare da jikkatar wasu uku.

Washegari da safe, yayin da ake jana’izar wanda ya rasu, wasu fusatattun matasa suka kai farmaki gidan sarkin Donga, suka jefa duwatsu suka fasa gilashin gidan, wanda hakan ma ya haifar da sake rasa rai daya.

Wasu mazauna yankin sun danganta tsayin daka da sarkin ke yi da wata ziyara da wani babban sarki ya kai masa a ranar Jumu’a, inda aka shimfiɗa masa sallaya a masallacin, amma ya ƙi yin sallah a ciki bayan ya ji cewa masallacin na Izala ne.

A halin da ake ciki, hukumomi da shugabannin addini suna kira da a rungumi zaman lafiya, tare da barin masallacin ga kungiyarsa ta Izala domin cigaba da ibada kamar yadda aka saba.

Allah Ya ba mu zaman lafiya mai dorewa.

Follow Us