Babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarni ga jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) da ta dakatar da shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da aka tsara a watan Nuwamba mai zuwa.
Rahoton Daily Trust ya ce Mai Shari’a James Omotosho ne ya bayar da wannan umarni, bayan karɓar ƙorafin wasu mambobin jam’iyyar guda uku da ke goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike.
Masu shigar da ƙarar sun nemi kotun ta hana PDP ci gaba da shirye-shiryen taron da aka tsara gudanarwa a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, suna mai cewa jam’iyyar ta karya dokokinta da kuma Dokar Zaɓe ta 2022.
Lauyan masu ƙorafi ya bayyana cewa PDP ta kasa gudanar da zaɓen shugabanni a jihohi 14 na ƙasar, abin da ya ce ya saɓa wa tsarin mulkin jam’iyyar.
A cewar rahoton, an yi zargin cewa sakataren jam’iyyar na ƙasa — wanda ke cikin sahun magoya bayan Wike — ya kai ƙara ga hukumomin tsaro, yana zargin shugabancin PDP da yin amfani da sa-hannunsa ba tare da izini ba, a wata takarda da aka aika wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) don sanar da taron. Sai dai PDP ta musanta wannan zargi, tana mai cewa dukkan matakan da aka ɗauka bisa doka ne.
Idan aka gudanar da taron, ana sa ran wakilan jam’iyyar za su zaɓi sabon shugabancin ƙasa, wanda ka iya bai wa bangaren da ke adawa da Wike damar sauke dukkan masu yi masa biyayya daga mukaman da suke rike da su.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin cikin gida ke ƙara kamari a jam’iyyar PDP, musamman tsakanin magoya bayan Wike da sauran shugabannin jam’iyyar na ƙasa.