Rahoton Musamman: Tattaunawa da Fulani a ƙananan hukumomin Jibiya, Batsari, Dutsinma da 'Yan tumaki

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes01112025_085941_FB_IMG_1761987576009.jpg



Wakilan jaridar Katsina Times sun shafe makonni suna gudanar da bincike a kasuwannin Jibia, Batsari, Dutsin-ma da ‘Yan Tumaki, cikin ƙoƙarin samun tattaunawa da wasu Fulani da suka fito daga dazukan da aka cimma yarjejeniyar sulhu da su, da kuma wasu Fulani masu ɗauke da makamai.

Bayan dogon ƙoƙari, wakilanmu sun samu damar yin magana da wasu daga cikinsu da suka fito daga cikin daji domin gudanar da cinikayya a kasuwa.

Za mu gabatar da cikakken rahoto nan gaba, insha Allah, tare da wasu hotuna da muka ɗauka cikin tsattsauran sirri.

Mun zabi hanyar tattaunawa da su a kasuwa ba tare da an shirya musu tambayoyi ba, domin mu ji abin da ke cikin zuciyarsu kai tsaye, da kuma gaskiyar fahimtarsu kan al’amuran da ke gudana.

Katsina Times
 Jaridar Taskar Labarai
 www.katsinatimes.com
 Facebook: Katsina City News 
 Dukkan shafukan sada zumunta: @Katsina Times
 0704 377 7779

Follow Us