Katsina Times
Taron matasan jam’iyyar APC na fadin Jihar Katsina na gab da gudana, inda ake sa ran zai haska muhimman ayyukan raya ƙasa da gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON ke gudanarwa.
Mai taimakawa Gwamnan Katsina kan kafafen yaɗa labarai na zamani, Hon. Abubakar Sani Ɗan Abba, shi ne ke jagorantar shirye-shiryen wannan gagarumin taro, wanda nufinsa shi ne faɗakar da matasa kan manyan nasarorin da Gwamna Radda ya cimma cikin sama da shekaru biyu kacal na wa’adinsa.
An tsara gudanar da taron a ƙarshen watan Nuwamba, 2025 a cikin garin Katsina, inda za a taro matasa daga kowane lungu da saƙo na jihar domin tattauna makomar su da kuma fahimtar irin ci gaban da gwamnati ke shimfiɗawa a fannoni daban-daban.
A yayin taron, matasan za su samu damar ganawa da mataimakan musamman na Gwamna tare da isar da saƙonninsu kai tsaye zuwa ga Gwamnan jihar.
Haka kuma, za a baje kolin ayyukan Gwamna Radda a fannoni daban-daban na rayuwa, tare da jawaban malamai da jiga-jigan siyasa domin ƙara wayar da kan matasa kan muhimmancin rawar da za su taka wajen cigaban jihar da makomar su.
Hon. Abubakar Sani Ɗan Abba, wanda shi ne Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Katsina kan Kafafen Sadarwa na Zamani, ya bayyana cewa taron zai zama dama ga matasa su gane irin nasarorin da gwamnati ke aiwatarwa a fadin jihar da kuma rawar da za su taka wajen dorewar cigaban da aka samu.