Manoma a dajin Kauyen Danchafa a Katsina sun koka da yunkurin karɓe gonakinsu da sunan gwamnati.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes03112025_183806_FB_IMG_1762194954970.jpg

Katsina Times 


Wasu manoma a dajin kauyen Danchafa, da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, sun koka kan abin da suka bayyana a matsayin yunkurin wani mutum mai suna Dikko Ladan, wanda suka ce na kusa da Gwamnan jihar Malam Dikko Umar Radda ne, na karɓe gonakinsu da sunan cewar wai gwamnan ne ya ba shi wurin.

Manoman, waɗanda ke noma a tsakanin kauyukan Ginzo, Danchafa da Kankare (yankin Arewaci da Yammacin Waya) sun bayyana damuwarsu ne ga jaridar Katsina Times a ranar Litinin, yayin wata ziyarar gani da ido da suka kira ta.

Shugaban ƙungiyar manoman, Injiniya Aminu Musa Lawal, ya ce sun kashe miliyoyin naira wajen gyara dajin da a da rukukin daji ne mai barazana ga rayuka, kafin su mai da shi gonaki masu amfani.

“A da daji ne. Muka zo muka gyara shi, muka kai taki. Yanzu wurin ya zama abin dogaro ga dubban mutane. Matasa daga kyauyukan yankin suna samun aiki ta hanyar yi mana noma da sauran ayyukan gona.” in ji shi.

Ya ƙara da cewar ba kawai sun mallaki wurin ne haka kawai ba, domin sun nemi izini daga hukumomin da ke da hurumi tare da samun takardun hakan, kuma suna biyan haraji duk shekara.

Sai dai a cewarsa duk da haka, kawai sai ga Dikko Ladan ya bayyana a rana tsaka yana shata fili da saka alamomi a kan gonakinsu na, yana cewa wai gwamna ne ya ba shi.

“Wurin da sama da mutane dubu biyu ke nomawa, yanzu mutum ɗaya kawai ake cewa za a ba shi. Ina da gona da nake noma damen dawa 50 zuwa 70 kowace shekara. Ban yarda wannan umarni daga gwamna Radda yake ba, domin ina ganin ba daidai ba ne; shi kuma na san shi mutum ne mai adalci da muradin ha6aka noma,” in ji Injiniya Musa.

Manoman har wayau, sun roƙi gwamnan jihar Katsina da ya shiga cikin lamarin domin bincike da tabbatar da adalci, suna masu cewa abin mamaki ne gwamnati ta bai wa mutum ɗaya tal fili mai faɗin hekta 500 da gonakin da ake noma a ciki da sunan daji, alhali akwai gonakin jama’a a ciki.

“Mun sha wahala wajen gyara wannan wuri shekaru da dama, don haka ya dace gwamnati ta saurari ɓangarorin da abin ya shafa.” in ji wani manomi daga cikinsu.

Da muka tuntu6i Dikko Ladan ta hannun wakilinsa, Alhaji Kabir, don jin ta bakinsa game da zarge-zargen manoman, ya bayyana cewa babu abin da zai iya cewa kan batun, amma a tuntu6i Hukumar gandun daji wato Forestry don karin bayani

Follow Us