Katsina Times
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da rabon buhunan hatsi 90,000 ga gidajen da ke cikin mawuyacin hali a faɗin jihar, a wani yunkuri na yaƙi da yunwa da ƙarancin abinci da ke addabar yara da iyalai.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke Katsina, inda Gwamna Radda ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da yunwa, wanda ya ce abu ne na wajibi da hakki ga reshi a matsayin gwamnan Katsina.
“Wannan aiki ba wai kawai batun abinci ba ne; al’amari ne na tausayi da nauyi da kuma alhakin da muke duka da shi,” in ji shi. “Mun kuduri aniyar ganin babu iyali a Katsina da zai kwanta da yunwa, kuma babu yaro da zai ci gaba da fama da ƙarancin abinci”
Ya bayyana cewa wannan shirin ya samo asali ne daga rahoton kwamitin bincike da ya kafa tun farkon shekara domin tantance matsalar ƙarancin abinci a jihar. Rahoton kwamitin, a cewarsa, ya gano matsaloli masu tayar da hankali da suka sa aka gaggauta daukar matakin gwamnati.
Gwamna Radda ya ce an tantance wadanda za su amfana da hatsi ta hanyar amfani da sahihan bayanai daga Hukumar Kula da Lafiyar a matakin Farko ta Jihar Katsina (PHCDA), kwamitocin al’umma da kuma kwamitin yaki da ƙarancin abinci domin tabbatar da gaskiya da adalci.
“Yin kulawa da yaranmu ba kawai nauyin dan kasa ba ne, wajibi ne na addini,” in ji shi. “Idan yaro ya ji yunwa, ko uwa ta kasa ciyar da jaririnta, ba matsalar tattalin arziki ce kawai ba, wani wajibi ga shugabanni su magance wannan matsala”
Gwamnan ya kuma bayyana wasu shirye-shiryen da ke gudana na inganta lafiyar yara da mata masu juna biyu a faɗin jihar. Ya ce gwamnatinsa tana kafa cibiyoyi 60 na Outpatient Therapeutic Programme (OTP) da kuma sabunta cibiyoyi 9 da ake kula da yara masu ƙarancin abinci a yankuna masu fama da matsalar.
Haka kuma, ya bayyana cewa gwamnati na shirin kafa masana’antar Tom Brown da Ready-to-Use Therapeutic Food (RUTF) a Katsina, domin samar da abinci mai gina jiki ga yara da mata masu shayarwa.
A cewarsa, wadannan shirye-shirye sun riga sun rage yawan yaran da ke fama da ƙarancin abinci a jihar zuwa kashi 8 zuwa 10 cikin ɗari.
Gwamna Radda ya ce rabon hatsi na daga cikin manyan shirye-shiryen gwamnati na kare marasa ƙarfi da tabbatar da tsaron abinci, wanda ya haɗa da tallafa wa manoma 4,000 da suke yin noman rani a karkashin shirin Katsina State Community Development Programme (CDP).
Ya yaba wa kwamitin yaki da ƙarancin abinci, shugabannin gargajiya da na addini, da abokan haɗin gwiwa irin su Médecins Sans Frontières (MSF) bisa goyon bayan da suke bai wa gwamnati wajen yaki da yunwa.
“Yayin da muke kaddamar da wannan rabon, ina kira ga duk wanda ke da hannu a cikin aikin da ya yi gaskiya da rikon amana. Kowanne buhu ya kai hannun wanda ya fi bukata,” in ji shi.
A nasa jawabin, Shugaban Kwamitin Ƙarancin Abinci, Dakta Ahmad Musa Abdullahi, ya bayyana wannan shiri a matsayin alamar tausayi da hangen nesa na Gwamna Radda.
Ya ce tun bayan kammala rahoton su a watan Satumba 2025, Gwamna ya amince da shirin nan take, wanda ya kai ga wannan rabon hatsi.
“Wannan aiki ba kawai jin kai ba ne; aiki ne na imani da ibada a gaban Allah,” in ji shi. “Kowane buhu da ake rabawa yau yana wakiltar abinci, fata, rahama da amincin jama’a ga Gwamnati.”
Ya tabbatar da cewa za a gudanar da rabon cikin gaskiya da bin doka, tare da sa ido daga hukumomi, shugabannin gargajiya da na addini, ALGON, da kwamitocin Zakka da Waqf.
Shugaban Shirin Ci gaban Al’umma (CDP), Dakta Kamal, ya ce wannan bikin ya zo daidai da cikar shekara ɗaya da shirin ke aiwatar da ayyukansa. Ya bayyana cewa CDP ta taimaka wajen inganta rayuwar dubban jama’a a fannin noma, abinci, da rage talauci.
“Manufarmu ita ce kai ci gaba kai tsaye zuwa ga al’umma,” in ji shi. “Muna godiya ga Gwamna Radda saboda hangen nesansa da jagorancin da yake bayarwa.”
Sakataren Hukumar Lafiya matakin Farko ta Jihar Katsina, Dakta Shamsuddeen Yahaya, ya bayyana shirin a matsayin sakamakon jajircewar Gwamna wajen tafiyar da harkokin lafiya da abinci mai gina jiki.
A nasa jawabin, Shugaban Ƙaramar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad, ya gode wa Gwamna saboda zaben Katsina a matsayin wurin farko da aka kaddamar da shirin, inda ya tabbatar da cewa kowace mazaba za ta samu rabonta.
Mataimakin Shugaban ALGON na Jihar Katsina, Hon. Rabo Tambaya, wanda ya wakilci sauran shugabannin ƙananan hukumomi 34, ya bayyana wannan shiri a matsayin na uku cikin jerin irin waɗannan tallafin da gwamnati ta aiwatar.
Ya ce, “Mun shaida canji mai kyau a rayuwar jama’a, kuma muna tabbatar da cikakken goyon baya domin ganin wannan shirin ya kai ga duk mai bukata.”
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin gargajiya da na addini, wakilan masarautun Katsina da Daura, abokan haɗin gwiwa kamar MSF, da kuma jama’ar da za su amfana daga sassa daban-daban na jihar.