Dambazau Ya Zargi Amurka da Shirya Kafa Sansanin Soji a Najeriya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes05112025_080022_FB_IMG_1762329461887.jpg



Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (mai ritaya), ya zargi gwamnatin Amurka da neman kafa sansanin soji a Najeriya.

Dambazau ya bayyana haka ne a wani taro da aka gudanar a Abuja, inda ya ce zargin wariyar addini da wasu ‘yan siyasa da shugabannin addini daga Amurka ke yadawa, yana da nasaba da wannan muradi.

Ya ce hakan na da alaka da kalaman tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya bayyana Najeriya a matsayin “kasa mai damuwa” tare da umartar Ma’aikatar Tsaron Amurka da ta dauki matakai don kare Kiristoci a Najeriya.

Dambazau ya yi bayanin cewa matsalar ta’addanci a Najeriya ba ta ta’allaka ga addini guda ba, domin duka Musulmi da Kiristoci na fuskantar barazana iri daya. Ya ce an sha samun hare-hare a masallatai, kisan malamai da sarakunan gargajiya a Arewa, wanda ke nuna cewa matsalar ta shafi kowa da kowa.

Tsohon hafsan sojin ya kuma nuna damuwa cewa wasu al’ummomi a jihohin Zamfara da Katsina sun shiga yarjejeniya da ‘yan bindiga domin neman kariya, wanda ya bayyana a fili gazawar gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Follow Us