Gwamnatin Katsina ta kaddamar da aikin jawo ruwan sha da zai ratsa kananan hukumomi shida na jihar.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes05112025_154141_FB_IMG_1762357291296.jpg



Auwal Idan Musa | KatsinaTimes 

Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da wani muhimmin aiki na jawo ruwan sha daga madatsar ruwa ta Zobe, wanda zai ratsa kananan hukumomi guda shida a jihar, domin samar da ruwan sha ga dubban jama’ar jihar.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a ranar Laraba a garin Kafin-Soli da ke karamar hukumar Kankia, inda Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya jagoranta.

A cikin jawabinsa, Gwamna Radda ya bayyana cewa aikin, wanda ake aka kira da Zobe Water Supply Project Phase 1B, zai ratsa kananan hukumomi guda shida da suka haɗa da: Dutsinma, Kankia, Charanci, Rimi, Batagarawa da Katsina.

 “Wannan Dam na Zobe shekaru 47 ke nan da kammala ta." In ji shi

Ya ce: "An fara shi a zamanin Shagari, aka bude shi a lokacin Buhari, yau kuma Allah ya kawo mu domin mu kaddamar da aikin Phase 1B." In ji Gwamnan.

"Za a ja ruwa daga Zobe Dam zuwa wadannan kananan hukumomi guda shida,” in ji Gwamna Radda.

Ya ce aikin zai lakume kimanin Naira biliyan 31, inda gwamnatin jihar ta riga ta biya kashi 40 cikin 100 na kudin aikin ga kamfanin da zai gudanar da shi.

An bayyana Mutual Commitment Company Limited (MCC) a matsayin kamfanin da zai aiwatar da aikin, tare da alƙawarin kammala shi cikin shekara guda.

Garuruwa da dama tare da dubban mutane da suka fito  daga kananan hukumi 6 din ne za su amfana da aikin, cewar Gwamnan, da suka hada da:Dutsin-ma, Karofi, Radda, Kafin-Soli, Tafashiya, Kankiya, Koda, Charanci, ‘Yar Randa, Tashar ’Yan Albasa, Are, Ci-ka-koshi, Kaduma, Tudun Kadir, Rijiyar Mai Siminti, Lambar Rimi, Abukur, Tashar Bala, Batagarawa da Birnin Katsina.

Gwamnan ya jaddada cewar, aikin zai amfani miliyoyin jama’a ta hanyar samar da ruwan sha mai tsafta da rage matsalar karancin ruwa a yankunan.

Bikin kaddamarwar dai ya samu halartar sarakunan gargajiya, jami’an gwamnati, ‘yanjarida, jami’an tsaro da dubban al’umma daga sassa daban-daban na jihar.

Follow Us