FRSC ta shirya gangamin wayar da kai kan matsalolin tuki a Katsina.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06112025_165146_FB_IMG_1762447848779.jpg



Auwal Isah | KatsinaTimes 

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Ƙasa (FRSC) reshen Jihar Katsina, ta shirya taron gangamin wayar da kai, tattaunawa da jin ra'ayoyin jama’a tare da masu ruwa da tsaki kan matsalolin tuki da ke haddasa asarar rayuka da dukiyar al’umma, a wani ɓangare na bikin wayar da kai na wasu watannin shekara (Ember Months Campaign) na 2025.

Taron, wanda aka gudanar a dakin taro na Bello Kofar Bai da ke Sakatariyar Jihar Katsina, an yi masa ya take da “Dauki alhakin tsare kanka; daina tukin da ke dauke hankali.”

A yayin jawabin bude taron, Kwamandan FRSC na Jihar Katsina, Corps Commander Maxwell Kaltungo Lede, ya bayyana cewar manufar taron shi ne jaddada wa kowane mai amfani da hanya cewar shi ne mai alhaki wajen kare rayuwa da rage haɗurra a hanya.

"Manufar wannan taro ita ce haifar da sauyin hali, ƙarfafa haɗin gwiwa da tabbatar da cewa kowane direba da mai hanya ya ɗauki alhakin tsaronsa. Muna fatan kowane tafiya ta kasance lafiya, kowane rai ya zama mai daraja,” in ji Kaltungo.

Ya ce, tuki cikin rashin kulawa na daga cikin manyan dalilan da ke jawo haɗurra a hanyoyin ƙasar, inda ya jero wasu daga cikin abubuwan da ke haddasa haka, kamar amfani da waya yayin tuki, fira da fasinjoji, cin abinci yayin tuki, damuwa, shan miyagun ƙwayoyi, gudu fiye da ƙima, da kuma gajiya.

Kaltungo, ya bayyana cewar daga watan Janairu zuwa Satumba na 2025, Njeriya ta samu haɗurra 7,715 (karin kashi 10.04% idan aka kwatanta da 7,011 na shekarar 2024).

Ya ci gaba da cewar, haka kuma, adadin mutanen da suka ji rauni ya ƙaru daga 22,373 zuwa 24,674 (karin kashi 10.28%), yayin da wadanda suka mutu suka karu da kashi 2.73% daga 3,811 zuwa 3,915.

Ya karanda cewar, sai dai a jihar Katsina, kwamandan ya ce an samu raguwar haɗurra, inda daga watan Janairu zuwa Oktoba 2025 aka samu haɗurra 70 kacal, raguwar kashi 39% idan aka kwatanta da 114 a 2024.
Haka kuma, mutanen da suka ji rauni sun ragu da kashi 7.6%, yayin da adadin mutuwa ya sauka da kashi 20% daga 123 zuwa 98.

Kaltungo ya gode wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, bisa irin kokarin gwamnatinsa wajen gyaran hanyoyi da inganta harkokin sufuri, yana mai cewar hakan na taka rawa wajen rage haɗurra da tabbatar da tsaro ga direbobi da fasinjoji.

A nasa jawabin, Gwamna Dikko Umaru Radda, wanda ya samu wakilcin Darakta-janar na Hukumar Kula da Tsaro da Zirga-zirgar Hanya ta Jihar Katsina (KASSAROTA), Manjo Garba Yahaya Rimi (mai ritaya), ya bayyana goyon bayan gwamnati ga irin wannan shiri da ke taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ya kwatanta direba da mai doki, yana mai cewar “Rayukanmu da lafiyarmu suna hannun wanda ke rike da sitiyari. Idan direba ya kasa sarrafa abin hawansa da kyau, hakan na iya kai shi ga halaka. Don haka wajibi ne kowa ya kula da abin da ke hannunsa.” In ji shi

Gwamnan ya bukaci masu ababen hawa da su rika bin dokokin hanya da kiyaye ka’idojin tuki don kaucewa haɗurra, yana mai cewar, “Mu tabbata mun kare rayukan mutane, dukiyoyinsu da lafiyarsu.”

A yayin taron dai, an gabatar da jawabai, tsokaci da shawarwari daga jami’an tsaro, Malaman addini, Malaman Manyan Makarantu, kungiyoyin direbobi, da sauran masu ruwa da tsaki a harkar. Daga ƙarshe, mahalarta taron sun bukaci kungiyoyin sufuri da masu wa’azi a masallatai da coci-coci da su kara kaimin wayar da kan jama’a game da illolin tukin a cikin yanayi mai dauke hankali, da kuma rashin bin dokokin hanya.

An ce za a tura shawarwarin da aka tattara daga taron zuwa ga Hedikwatar FRSC domin mikawa Gwamnatin Tarayya don duba su.

Follow Us