Gwajo-Gwajo ya Yabawa Gwamna Radda kan Gina Kasafin Kudi Bisa Bukatun Al'umma

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes07112025_135611_FB_IMG_1762444293676.jpg

Mai Bada Shawara na Musamman ga Gwamna Dikko Umaru Radda kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ya'u Umar Gwajo-Gwajo, Ya yabawa gwamna bisa gina kasafin kudin jihar na shekarar 2026 bisa ra'ayoyi da bukatun al'ummar jihar.

Wata sanarwa da jami'in ya raba wa manema labarai a Katsina, ta lura cewa wannan shine karo na farko da aka kafa kwamitoci su zaga gundumomi 361 a jihar su tuntubi al'umma game da buƙatunsu don a saka su a cikin kasafin kuɗi.

Ya bayyana cewa ayyukan da al'ummomin suka nema sun fi bada karfi a kan batun ilimi, da kiwon lafiya, noma, manyan ayyuka, tsaro, muhalli, da sauran muhimman fannoni, da nufin inganta rayuwar al'ummomi a birane da karkara a jihar.

"Wannan shi ne karo na farko a tarihin Jihar Katsina da aka ba jama'a damar fada wa gwamnati abin da suke so a saka a kasafin kuɗi, kwamitoci aka kafa su je mazabu 361 dake fadi jihar nan su jiyo ra'ayoyin jama'a da buƙatunsu domin a saka musu shi a kasafin kudi.

"Wannan tsarin shi ake aiwatarwa a manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, sai sun shirya taron jin ra'ayoyin jama'a sannan suke shirya kasafin kudi bisa waɗannan buƙatun, kuma shine tsari mafi inganci wajen kawo ma al'umma cigaba

"Jama'a suna ta godiya da sambarka cewa a karo na farko an samu gwamnati da take fifita buƙatunsu a wajen tsara kasafin kudi, kuma da zarar shekarar ta kama zasu fara ganin aiyukan da suka bukaci a aiwatar a gundumominsu.

"PhD tayi aiki, an gabatar da ilimi wajen fitar da tsari da zai kawo ma al'umma cigaba kai tsaye, shi yasa kafin gwamnatin ta shekara biyu ta cikar ma al'umma duk alkawuran da tayi musu" in ji Gwajo-Gwajo.

Sanarwar ta bayyana cewa bangaren ilimi ya samu kaso mafi tsoka, sai bangaren kiwon lafiya, ayyuka, noma, habbaka masana'antu da sauran muhimman bangarori dake kunshe cikin kundin tsarin cigaba na gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda.

Ya ce nan da ƙarshen shekarar 2026, kowace cikin gundumomi 361 dake jihar za ta samu ayyuka uku zuwa huɗu a fannonin da suka fi buƙata domin a inganta rayuwarsubda tattalin arzikinsu.

Alhaji Ya'u Gwajo-Gwajo ya kuma yaba bisa yadda gwamnan ya ware kashi 81% na jimillar kasafin kuɗin ga manyan aiyuka a fannin ilimi da kiwon lafiya da sauransu, kashi 19% kuma na gudanar da harkokin gwamnati wanda yace ya fifita muhimman fannoni da za su yi tasiri kai tsaye ga rayuwar al'umma.

"Ya ware sama da kashi 80% na kasafin kuɗin ga kashe kuɗin ga manyan aiyukan a fannoni daban daban musamman ilimi, kiwon lafiya, noma, muhalli, habbaka masana'antu da sauran fannoni masu mahimmanci a ƙarƙashin tsarin cigaba na wannan gwamnatin.

"Ina kuma yaba wa 'yan Majalisar Dokokin Jihar Katsina bisa yadda suka tantance kasafin kuɗin a kan kari don a fara aiwatar da shi a watan Janairu na shekarar 2026," in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma yi kira ga al'ummar jihar Katsina da su ci gaba da ba gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda cikakken goyon baya don ta cika burinta na inganta rayuwar al'umma sa habbaka tattalin arzikin jihar.

Follow Us