Tafiyar Shugabannin Kananan Hukumomin jihar Katsina Ƙasar Ingila, ...Horon Sanin Makamar Aiki ko Wawushe Dukiyar Jama’a?

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09112025_131807_FB_IMG_1762694263587.jpg

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, Nuwamba 9, 2025

Tafiyar shugabannin kananan hukumomin Jihar Katsina zuwa birnin Liverpool na ƙasar Ingila domin halartar horon mako biyu ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, inda ake tambayar ko tafiyar za ta haifar da ɗa mai ido ko kuwa wata hanya ce ta ɓata dukiyar jama’a da sunan samun horo.

Rahotanni sun bayyana cewa shugabannin kananan hukumomin sun tashi daga filin jirgin saman Abuja a farkon wannan mako, inda aka bayyana manufar tafiyar a matsayin “shirin inganta jagoranci da gudanar da mulki” domin ƙara kwarewar shugabanni a matakin ƙananan hukumomi.

Sai dai tafiyar na zuwa ne a lokacin da al’umma ke cikin ƙunci na tattalin arziki da matsalolin tsaro a yankunan karkara.

Wasu daga cikin ‘yan ƙasa da masu fashin baki sun bayyana tafiyar a matsayin “bata lokaci da asara ga gwamnati.”
Malam Abdullahi Sule, masani kan al’amuran yau da kullum a Katsina, ya ce:

“Shugabanni ne waɗanda kamata ya yi su kasance a cikin al’umma suna warware matsalolin tsaro da yunwa, amma sai ga su suna daukar hoto a filin jirgi suna nufar Ingila. Me zai canza cikin sati biyu da za su yo a can?”

A shafukan sada zumunta kuwa, hotunan da aka gani na shugabannin suna shirye-shiryen tafiya sun jawo tsogwamin  jama’a, inda da dama suka bayyana tafiyar a matsayin wata hanya ta yin yawo da kuɗin gwamnati kawai.

Wani jami’i daga ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Katsina da ya so mu sakaya sunan sa ya kare shirin, yana mai cewa:

“Wannan tafiya wani ɓangare ne na shirin gwamnati na sabunta tsarin mulki da ƙara wayar da kan shugabanni kan yadda ake tafiyar da mulki bisa ƙa’ida.”

Ya ce an ware kuɗin tafiyar cikin kasafin kuɗi, kuma an amince da su a majalisar zartarwa.

“Ba za mu iya ci gaba da zama cikin duhu ba. Shugabanninmu suna bukatar ganin yadda ake gudanar da mulki a ƙasashe masu cigaba,” in ji shi.

Masana harkar gudanar da mulki sun raba ra’ayi kan amfanin irin waɗannan horo na ƙasashen waje.
Dr. Jidda Abubakar wata malamar Jami'a ta ce, horo abu ne mai kyau amma yawanci ba ya kawo canji kai tsaye.

 “A mafi yawan lokuta, irin waɗannan tafiye-tafiye ba su da tasiri kai tsaye a aikace. Ba tare da tsarin aiwatarwa bayan dawowa ba, suna zama irin yawon siyasa ne kawai.”

Ta ƙara da cewa gwamnati za ta iya gudanar da irin wannan horo a cikin ƙasar nan, ta hanyar haɗin gwiwa da jami’o’i ko cibiyoyin koyarwa na cikin gida domin rage kuɗi da kuma amfani da masana na gida.

Tafiyar ta sake haifar da muhawara kan yadda jami’an gwamnati ke amfani da kuɗin jama’a wajen yin balaguro zuwa ƙasashen waje, musamman a lokacin da ake fama da yunwa, talauci da matsalar tsaro.

Wasu kungiyoyin fafutuka na ganin saka ƙa’idoji masu ƙarfi da tsarin lissafin amfanin irin waɗannan horo kafin a kashe kuɗi masu yawa.

Yayin da tawagar shugabannin ke kan hanyar su ta Liverpool domin karbar horo na sati biyu, ra’ayoyin jama’a sun kasu biyu. Wasu na ganin dama ce ta koyon dabarun mulki, yayin da wasu ke ganin wata hanya ce ta ƙetare dukiyar al’umma.

Ko wannan horo zai haifar da gyara a ayyukan gundumomi bayan dawowarsu, ko kuma zai zama wani sabon labari na “tashin jirgi da dawo da dawowa kawai,” lokaci ne zai tabbatar.

Follow Us