KASSAROTA Ta Kama Motar Sata A Mai’adua

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11112025_185917_FB_IMG_1762887528683.jpg



Hukumar Kula da Tsaro da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA), reshen Mai’adua, ta samu nasarar kama wata motar da ake zargin sata ce, kirar Peugeot 406 mai launin ja, yayin da jami’anta ke gudanar da sintiri a yankin karamar hukumar Mai’adua.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 9 ga watan Nuwamba, 2025, lokacin da jami’an Kassarota suka hango motar cikin hali na zargi. Bayan sun bi sahun motar, daga bisani suka gano cewa an sata ta.

Bayan kammala bincike na farko, hukumar ta mika motar da masu tuhumar ga rundunar ‘yan sanda ta Mai’adua domin ci gaba da bincike kan yadda aka sace ta da kuma wadanda ke da hannu a cikin lamarin.

Shugaban Hukumar Kassarota ta Jihar Katsina, Major Garba Yahaya Rimi (Rtd), ya jinjinawa jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai cewa wannan babbar nasara ce ga hukumar da kuma jihar Katsina baki ɗaya. Ya bukaci jami’an da su ci gaba da aiki da gaskiya, rikon amana da jajircewa wajen kare dukiyar al’umma.

A nasa jawabin, Sakataren Hukumar, Aminu Lawal Batsari, ya gargadi jami’an da su rika zuwa aiki akai-akai, yana mai cewa hukumar ba za ta lamunci sakaci ko kin bin doka ba daga kowane jami’i. Ya kara da cewa hukumar na da tsari na musamman wajen ɗaukar mataki a kan duk wanda aka samu da sakaci.

Shi ma Commandant na Hukumar a matakin jiha ya tabbatar da cewa suna ci gaba da karɓar rahotanni daga dukkan shiyyoyi, tare da kira ga jami’ai da su kasance masu gaskiya da adalci a yayin gudanar da aikinsu.

A ƙarshe, Alhaji Dahiru Bagiwa, ya gode wa jami’an hukumar na shiyyar Daura bisa wannan gagarumar nasara da suka samu, yana mai cewa hakan ya nuna kwazo da amincin jami’an Kassarota. Haka kuma ya yaba wa Unit Commander, Nuraddeen Garba Rimi, bisa jajircewarsa wajen ganin an ceto motar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Abubakar Marwana Kofar Sauri, ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Follow Us