Gwamnatin Jihar Katsina Ta Nemi Hada Kai da Kungiyar ACF Don Samar da Ayyukan Yi Ga Matasan Jihar

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11112025_220539_Screenshot_20251111-230436.jpg



Gwamnatin Jihar Katsina ta bukaci hadin gwiwa da Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), reshen jihar, wajen samar wa matasan jihar ayyukan yi da kuma jawo masu saka hannun jari zuwa Jihar Katsina.

Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Faruk Lawal Jobe, ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, yayin da ya karɓi bakuncin zababbun jami’ai da dattawan kungiyar a Gidan Gwamnati na Katsina a yau.

Alhaji Faruk Jobe ya ce Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda na maraba da dukkan ayyukan alheri da Kungiyar ACF reshen Jihar Katsina ke gudanarwa. Ya kuma yaba da jagororin kungiyar, inda ya bayyana su a matsayin sanannu kuma nagartattun mutane a jihar.

Mataimakin Gwamnan ya bayyana irin kyawawan ayyukan da Gwamnatin Malam Dikko Umar Radda ke aiwatarwa a fadin Jihar Katsina, ciki har da bunkasa ilimi ta hanyar inganta hanyoyin koyarwa da daukar ma’aikata sama da dubu bakwai. Haka kuma, an samar da guraben karatu na fannoni na musamman ga matasa a kasashen waje tare
da biya musu dukkan hakkokinsu.

Sauran fannoni da Gwamnatin ta samu dimbin nasarori sun hada da samar da ruwan sha mai tsafta a birane da karkara, da kuma rarraba kayan noma da takin zamani ga manoma. Haka nan, gwamnati ta sabunta fasalin manyan birane da garuruwa a jihar, tare da fadada Cibiyar Horas da Sana’o’i ta Jihar Katsina domin tallafa wa matasa maza da mata wajen samun jarin gudanar da sana’o’i.

Alhaji Faruk Jobe ya sake nanata bukatar hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Katsina da Kungiyar ACF, reshen jihar, wajen samar wa matasa ayyukan yi da kuma jawo masu saka jari zuwa jihar.

A nasa jawabin, Shugaban Kungiyar ACF na Jihar Katsina, Alhaji Shehu Musa Malumfashi, ya bayyana wa Mataimakin Gwamna cewa a bara ne aka zabi zababbun jami’an gudanarwa na kungiyar, wadda a halin yanzu ke da mambobi sama da dari uku.

Ya kara da cewa daga cikin ayyukan da kungiyar ta gudanar akwai gangamin wayar da kan al’umma kan muhimmancin yin rijistar katin zabe da kuma kada kuri’unsu a lokacin zabe. Haka kuma, kungiyar ta kai dauki ga asibitoci a lokacin da aka fuskanci matsalar cututtukan zazzabin typhoid da na cizon sauro.

Alhaji Shehu Musa Malumfashi ya ce kungiyar ACF, reshen jihar, ta kuduri aniyar hada kai da gwamnati wajen bunkasa zaman lafiya da daukaka martabar Jihar Katsina. Ya kuma mika godiya ga gwamnati bisa kyakkyawar tarbar da aka yi musu.

A yayin ziyarar, Shugaban kungiyar ya mika wa Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Faruk Lawal Jobe, magungunan tallafi da mambobin Zauren ACF reshen Jihar Katsina suka samar domin kaiwa asibitoci kyauta, a matsayin gudunmuwar kungiyar wajen inganta harkar kiwon lafiya a jihar.

Cikin jami’an kungiyar da dattawan da suka hallarci taron akwai Sakataren Kungiya, Alhaji Bello Iro Dabai; Sakataren Watsa Labarai, Dr. Sada Salisu Rumah; Danwairen Katsina da Mataimakinsa, Alhaji Lawal Kasimu Funtua; Alhaji Abdu Halliru; Alhaji Tukur Lamami; Dr. Ahmed Ingawa; da Alhaji Murtala Maikudi.

Follow Us