Cibiyar IPI Ta Duniya Ta Ce Za Ta Sa Ido Sosai Akan Cin Zarafin ’Yan Jarida A Nijeriya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes03122025_103802_a_Convert_this_logo_to (4).png



Danjuma Katsina | Katsina Times

Kungiyar International Press Institute (IPI) reshen Najeriya ta bayyana cewa za ta tsaurara mataki wajen dakile duk wani sabon hari, barazana ko cin zarafi da ake yi wa ’yan jarida a ƙasar nan.

Shugaban IPI Nigeria, Musikilu Mojeed, ya bayyana haka a jawabinsa na maraba a wajen taron shekara-shekara na 2025 IPI Nigeria Conference and Annual General Meeting da aka gudanar a Abuja ranar Talata.

Taron ya samu halartar fitattun manyan baƙi, ciki har da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, wanda ya jagoranci zaman, da Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a Mohammed Idris.

Mojeed ya ce lokaci ya yi da za a dakile rashin hukunta masu aikata laifuka kan ’yan jarida. Ya nemi sake duba wasu dokoki da ake amfani da su wajen danniya, musamman dokar laifukan intanet da kuma tsofaffin dokokin ɓatanci.

Ya yi nuni da cewa: “Akwai wurare da yawa da ake amfani da ikon gwamnati wajen danniya kan ’yan jarida ba tare da hukunci ba. Idan laifuka kan ’yan jarida suka wuce ba tare da hukunta su ba, saƙon da ake turawa shi ne cewa rufe bakin kafafen yaɗa labarai abu ne da ake yarda da shi.”

Ya ce aikin jarida hidima ce ga al’umma mai haɗari, don haka ya kamata ’yan jarida su samu kariya da mutuntawa. Ya gargadi cewa daga yanzu duk wani hari a kan ’yan jarida za a tunkare shi da ƙarfi.

Mojeed ya ce Najeriya ta ba mataki 112 zuwa 122 a jerin ƙasashen duniya masu mutunta ’yancin ’yan jarida, kuma wannan ya faru ne sakamakon danniya da cin zarafi a jihohi daban-daban.

Ya ambaci misalai da dama na cin zarafin ’yan jarida, ciki har da:

Sa ido, kai musu hari, da tsare su ba bisa ƙa’ida ba.

Rufe gidajen yaɗa labarai saboda dalilan siyasa, kamar yadda aka rufe tashoshin NTA, Pride FM, Gamji TV da Al-Umma TV a Zamfara saboda watsa taron jam’iyyar adawa.

Tsoratar da masu aikin bincike, ciki har da sace ɗan jarida Segun Olatunji tare da daure shi da kai shi nesa da gidansa.

Amfani da dokar laifukan intanet wajen cafke ’yan jarida, duk da an gyara dokar.

A watan Agusta 2024 kaɗai, akalla ’yan jarida 56 aka kama ko aka kai musu hari yayin rufe zanga-zanga.

Mojeed ya ja hankalin ’yan jarida da su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya: “Idan an kama ɗan jarida a Kano, ya kamata wanda ke Akwa Ibom ya damu. Idan an kai hari ga dakin labarai a Neja, ya kamata Lagos ta yi magana.”

Ya ce aikin jarida ginshiƙi ne na dimokuraɗiyya. Idan an tsoratar da kafafen yaɗa labarai, zaɓe zai rasa inganci, rashawa za ta yawaita, rayuwa za ta ƙara ɓaci.

Ya roƙi gwamnatin tarayya ta dakatar da gwamnoni, jami’an tsaro da duk wani jami’in gwamnati da ke cin zarafi ko danniya ga ’yan jarida, tare da samar da ingantaccen tsarin kariya.

A ƙarshe, Mojeed ya tuna da marigayiya Rafat Salami, tsohuwar ma’ajiya ta IPI Nigeria, wadda duk da takura da ciwo, ta halarci taron bara tana aiki har ƙarshen ƙarfinta. Don karramarta, IPI za ta kafa gasa ta musamman a Jami’ar Abuja domin tunawa da jarumtarta da sadaukarwa ga aikin jarida.

Follow Us