Danjuma Katsina | Katsina Times
Ministan Yaɗa Labaran Nijeriya, Malam Mohammed Idris, ya bayyana cewa jarida mai zaman kanta, wadda ke aiki cikin ƙwarewa da tsanaki, ita ce ginshikin dimokuraɗiyya mai inganci.
Ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin taron shekara-shekara na ƙungiyar International Press Institute (IPI) Nigeria, wanda aka gudanar a Abuja.
A bikin budewa da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya jagoranta, Ministan wanda shi ne Bako na Musamman, ya ce taken taron na bana, “Magance Danniyar ‘Yan Jarida a Najeriya” ya wajaba a kwatanta shi da abubuwan da suka faru a baya da kuma yanayin da ake ciki yanzu.
Ministan ya ce: “Lokaci yayi da za mu zauna mu tantance gaskiyar al’amura. Shin wannan take na taron na nuni da halin da muke ciki a yau, ko kuwa yana makantar da mu ne kan wani irin lokacin da muke ƙoƙarin kaucewa? Idan take na nufin cewa gwamnati mai ci na aiwatar da wani tsari na danniya ga ‘yan jarida, to wajibi ne mu binciki hakan da hujjojin da ke akwai.”
Ya ce manufarsa ba wai lissafa nasarorin gwamnati ba ce, “sai dai bayar da hujjoji da shiga muhawara mai ma’ana game da irin tafarkin da muke bi domin gina dimokuraɗiyya mai ɗorewa da ingantacciyar doka.”
Idris ya nanata cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana aiki ne bisa ka’idar cewa jarida mai zaman kanta ita ce cibiyar da al’umma ke tattaunawa da kanta.
Ya ce: “Kokarin da muke yi na halartar wannan taro tare da Mataimakin Shugaban Ƙasa, wani sako ne na tabbatar da jajircewarmu ga wannan mahimmin tattaunawa.”
Ministan ya ce hukumomin tsaro yanzu suna aiki ne bisa tsauraran ka’idoji domin mutunta ‘yancin ‘yan jarida, musamman a wuraren rikici da yayin zanga-zangar jama’a.
Ya kara da cewa gwamnatin Tinubu na tabbatar da ingantaccen yanayi da zai bai wa kafafen yaɗa labarai damar bunƙasa cikin ‘yanci ba tare da tsoro ba.
Sai dai ya amince cewa kalubale na nan: “Daidaikun kasashe na fama da batun daidaita tsaro, yaƙi da labaran ƙarya da kuma kiyaye cikakken ‘yancin jarida.”
Ministan ya bada misalin yadda wata jarida ta wallafa labari na ƙarya cewa wata yarjejeniya ta tilasta Najeriya rungumar LGBTQ+. Ya ce labarin ya yi barazana ga hadin kai, saboda haka gwamnati ta tunkare shi ta hanyar bayyana gaskiya ba tare da tilastawa ko hukuntawa ba.
Ya ce: “Maimakon danniya, mun fitar da cikakkiyar yarjejeniyar domin jama’a su gani, muka yi bayanin ƙaryar, sannan muka kai ƙorafi ta hanyar Ombudsman mai zaman kansa. Wannan ya tabbatar da cewa gaskiya da bayanin daidai shi ne makamin kare ‘yancin jarida.”
Idris ya bayyana cewa Najeriya ce za ta karɓi hedikwatar cibiyar Media and Information Literacy (MIL) ta ƙasa da ƙasa. Ya ce cibiyar ba za ta zama muryar gwamnati ba, “sai dai wata cibiyar horarwa ta Afirka baki ɗaya domin inganta tunani, tantance bayanai, da ɗabi’ar aikin jarida.”
Ya ce wannan mataki “zuba jari ne na dogon lokaci domin wayar da kan al’umma da kare su daga barazanar labaran ƙarya.”
Ya gayyaci dukkan ƙungiyoyi da su halarta bikin kaddamar da cibiyar a farkon watannin shekarar 2026.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki tare da IPI, Kungiyar Editocin Najeriya (NGE) da NUJ wajen duba dokoki domin tabbatar da cewa suna kare ‘yancin faɗin albarkacin baki tare da kiyaye muradun jama’a.
Ministan ya ce: “Ina da tabbacin cewa zan ci gaba da zama muryar kare ‘yancin jarida a Majalisar Zartaswa ta Tarayya, tare da tabbatar da cewa muna tafiya kan ingantaccen shugabanci da budaɗɗen al’umma.”