KatsinaTimes
An kammala shirye-shirye domin gudanar da Gasar tseren Dawaki ta Doguru ta Kasa da Kasa na 2025, wadda Ameer Stable tare da haɗin gwiwar Hukumar Horse Racing Federation of Nigeria suke shyiryawa. Za a gudanar da taron daga 31 ga Disamba 2025 zuwa 3 ga Janairu 2026, a Filin Tseren Dawaki na Doguru, karkashin taken Renewed Hope.
A cewar masu shirya gasar, za a tantance sabbin dawaki a ranar Litinin 29 da Talata 30 ga Disamba 2025 da misalin ƙarfe 10:00 na safe. Sakataren Tseren Dawaki Ishaqa Aliyu Mustapha, ya shedawa manema labarai cewa takardun shiga za su tsaya ne ga dawaki ashirin (20) na farko da suka cika ka’idoji.
Za a samu fitattun ‘yan tseren doki da mashahuran stables daga sassan Najeriya da wasu kasashen waje. Kwamitin shirya gasar ya fitar da dokoki domin tabbatar da tsaro da adalci yayin tseren. Inji shi
An wajabta wa dukkan ‘yan tseren Dawakin su sanya cikakken kayan aikin jockey. Duk wani dan tseren da aka samu da shan miyagun kwayoyi ko barasa a ranar tseren za a dakatar da shi. Haka nan duk dokin da aka gano yana dauke da cuta mai yaɗuwa za a gaggauta cire shi daga gasar tare da killace shi daga sauran dawaki.
Kwamitin ya jaddada cewa ba za a karɓi wani koke ko gardama ta baki ba. Duk koke-koke ko kalubalantar hukunci dole a aiko a rubuce a tura su zuwa ga kwamitin gudanarwa.
Gasar Gudun Doki ta Doguru na daga cikin manyan al’adu kuma fitattun wasannin gargajiya a Najeriya, wadda ke jan hankalin masoya wasa, masu kiwon dawakai da mahalarta daga fadin Afirka ta Yamma.