Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Auwal Isah Musa (KatsinaTimes)
Wani gogaggen masanin lafiyar kwakwalwa da ya shafe sama da shekaru 40 yana aiki a Birtaniya da Najeriya, Shehu Dandaura Musa, ya bayyana damuwa kan karuwar shaye-shaye, yawan barin makaranta da kuma yadda wasu matan aure ko ‘yan mata ke yawan barin gida na kwanaki ko makonni a wasu sassan Arewacin Najeriya.
A tattaunawa ta musamman da ya yi da KatsinaTimes, Musa ya danganta mafi yawan matsalolin da ake gani a cikin iyalai ga yawaitar shan miyagun ƙwayoyi tsakanin matasa.
Ya ce mafi yawan al’amuran da yake fuskanta sun haɗa da samari da ‘yan mata da ke barin gida sakamakon tasirin miyagun abokai da kuma amfani da abubuwan maye. A cewarsa, ‘yan mata da dama yanzu na kwashe kwanaki ko makonni a wani waje ba tare da sanin Iyaye ba, sannan daga bisani su dawo bayan fuskantar yanayi mai haɗari.
“Wadannan dabi’u suna da alaƙa kai tsaye da shaye-shaye da kuma gurɓatattun abokai da ke yaudarar matasa da alkawarin rayuwa mai kyau a waje,” in ji shi. Ya kara da cewa zaman banza da rashin aikin yi na kara ta’azzara lamarin.
Shehu Dandaura Musa ya ce babu ingantattun alkaluma da ke nuna yawan matasan da ke barin gidajensu, domin masana na aiki ne kawai da bayanan da ake kawo musu, ba tare da wata babbar kididdiga ko bincike ba.
Ya shawarci iyaye da al’umma su rika neman taimako da wuri idan sun lura da wani canji a halin ‘ya’yansu, yana mai cewa rigakafin farko shi ne mafi tasiri.
“Yawanci ana kawo mana yara ne lokacin da abin ya soma bayyana ƙarara. Ya fi kyau a nemi taimako da wuri, kafin lamarin ya gagara,” in ji shi.
Musa ya bukaci iyaye, shugabanni da al’umma su rika tuntuɓar ƙwararru don samun shawarwari, bada horo ko kuma taimakon gyara dabi’a idan an fara ganin matsala, maimakon a jira matsalar ta yi tsanani.