Daga Aisha Aliyu
@ Katsina Times Media Group
Wani matashi tare da goyon bayan ’yan uwansa masu kishin jam’iyyar APC, sun shirya taron gangamin matasa domin bayyana ayyuka, nasarori da kuma jaddada goyon baya ga gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa, PhD.
Taron, wanda aka tsara gudanarwa a ranar Lahadi, 14 ga watan Disamba, 2025, a ɗakin taro na Continental Computers da misalin ƙarfe 10 na safe, ya samu ɗaukar hankalin jama’a tun kafin lokacin gudanar da shi.
Nazarin da Katsina Times ta gudanar ya gano cewa wannan taro shi ne irin sa na farko a jihar Katsina, kuma ɗaya daga cikin sabbin dabarun da aka fara gani a wasu jihohin da jam’iyyar APC ke jagoranci a Nijeriya. Wannan ya ƙara mayar da Katsina abin koyi wajen shirya tarukan matasa masu ma’ana da tasiri.
Taron, wani muhimmin ƙoƙari ne da matasan suka ƙirƙira domin bayyana ayyukan gwamnatin APC da kuma nuna goyon bayansu, tare da faɗakar da al’umma kan irin ayyukan alheri da gwamnati ta aiwatar. Haka kuma taron ya yi niyya ne wajen zaburar da matasa domin su zama masu aiki da tasiri a cikin jama’a, maimakon zama ’yan kallo ko masu bin ofisoshi neman buƙatu.
Haka zalika, taron ya kasance dandalin haɗin kan matasan APC a inuwa ɗaya domin fuskantar ayyukan da ke gabansu, musamman na kare martabar jam’iyya da sake gabatar da ita ga al’umma kafin zaɓen 2027.
Ɗaya daga cikin manyan nasarorin taron shi ne yadda shugabanni, dattawa, da matasan jam’iyyar APC suka nuna cikakken goyon baya ga wannan yunƙuri.
Har ila yau, masu goyon bayan gwamnatin Malam Dikko Raɗɗa, PhD, da masu kishin cigaban jihar Katsina sun nuna farin ciki da fatan samun gagarumar nasara.
Abin burgewa, matashin da ya kafa wannan taro, tare da taimakon abokansa, matashi ne mai tarihin hidima ga jam’iyyar APC tun kafin ta karɓi mulki.
Ya bayar da gudunmawa wajen tallata jam’iyya a lokutan ƙalubale, kuma wannan taro ya kasance ɓangare ne na ci gaba da wannan hidima.
Taron ya zo a daidai lokacin da Gwamnan Katsina ya kammala zagayen ƙananan hukumomi 34 domin ƙaddamar da ayyuka da ganawa da al’umma.
Ana sa ran cewa a ranar taron, Gwamnan da wasu muƙarrabansa za su gana da matasa tare da jaddada goyon bayan gwamnati ga cigaban matasa a jihar.
Yadda aka kwashe kwanaki ana tallata taron ya jawo hankalin jama’a ƙwarai, kuma ana hasashen taron zai kasance ɗaya daga cikin tarukan matasa mafi tasiri a jiharsa cikin shekarar 2025.