Fashewar Bam ta jikkata mutane da dama a jihar Zamfara

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12122025_165727_FB_IMG_1765558542600.jpg


Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan wasu bama-bamai da ake zargin ‘yan bindiga suka ɗana  a kan hanyar Gurusu zuwa Gwashi da ke karamar hukumar Bukkuyum.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, da misalin ƙarfe 8:32 na safe, inda ya rutsa da wata motar Toyota, da ke dauke da fasinjoji daga yankin Gwashi. 

Rahoton mai sharhi a kan sha'anin tsaro Zagazola Makama, ya ce sojojin Operation Fansān Yamma tare da kwararrun masu lalata bama-bamai sun isa wurin domin gudanar da bincike.

Har yanzu ba a tabbatar da adadin wadanda suka jikkata ba, domin jami'an tsaro na cigaba da aikin tantance abin da ya faru.

Ana zargin cewa wannan harin na da alaka da wani fitaccen shugaban ‘yan bindiga, Sadiku, wanda ke aiki tare da gungun Dogo Gide.

Ba'a samu damar jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan Zamfara, Yazid Abubakar, ba a lokacin hada wannan rahoto.

Follow Us