A KADDAMAR DA DOKAR TA BACI KAN TSARO-DATTAWAN AREWA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11062026_095514_829b3c89-030e-4ced-89ac-54308a7f0a77_cx0_cy13_cw0_w1080_h608_s.jpg


Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi 

Zauren Taron Dattawan Arewa ya bukaci gwamnatin tarayya a kan ta kaddamar da dokar ta baci a kan matsalar tsaro, kasancewar Najeriya na fuskantar wani irin kalubalen tsaro da ke barazana ga cigaban tattalin arziki da zamantakewar jama'a.


Zauren Taron Dattawan, a cikin wata sanarwa da su ka fitar dauke da rattaba hannun Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya bayyana damuwa a kan yadda a ke fuskantar durkushewar sha'anin tsaro, a in da jama'a ke rayuwa cikin zullumi Yan ta'adda Kuma na kara fitowa gaba-gadi.


Zauren Taron ya ambato sashe na 14 (2) (b) na kudin tsarin mulkin Najeriya da ya ce wajibi ne kare rayuka da dukiyoyin jama'a ya zama nauyi a wuyan gwamnati, sai ya kalubalanci dalilin da ya sa a ka bar mutane su nemawa kan su mafita daga barazanar Yan bindiga da ma su garkuwa da mutane da sauran nau'oin yan ta'adda daban-daban.


Dattawan sun bayyana cewa Najeriya ta fuskanci matsalolin tsaro iri-iri a baya kamar su yakin basasa da rikicin Mai Tatsine da Ma su Tayar da Kayar Baya a Yankin Neja Delta, to amma abubuwan da ke faruwa yanzu sun Sha banban matuka, duba da yadda ayyukan ta'addanci kala-kala ke cigaba da bazuwa kusan a kowane yanki da bangare na kasar nan.


Zauren Taron Dattawan ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki tsauraran matakai a kan wadannan matsaloli, ciki har da sake salon tattarawa da amfani da bayanan sirri a tsakanin hukumomin tsaro, da yakar Yan bindiga gami da hukunta ma su daukar nauyin ayyukan laifi babu sani babu sabo.


Sauran shawarwarin da Dattawan na Arewa su ka bayar sun hada da yin binciken dukkanin wuraren da a ke aikata haramtaccen aikin hako ma'adanai a kasar nan, da kara karfafa tsaro ga manoma da makarantu da bangaren sufuri, da Kuma tabbatar da yin abinda ya dace a bangaren kashe kudade a kan ayyukan tsaro.


A yayin da zauren Taron ke bayyana matsalar tsaro a matsayin matsalar kasa baki daya ba wai wani bangare guda ba, ya ce yadda da amincewar da al'umma su ka yi wa gwamnati za ta cigaba da zaizayewa madamar ba a dauki matakai a kan wadannan matsaloli ba.

Follow Us