Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta kasa ta gudanar da taron Majalisar Zartaswarta a dakin taro na Jami’ar Assalamu Global University, mallakin Kungiyar, da ke garin Hadejia a Jihar Jigawa.
Taron ya gudana ne karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar na kasa, kuma Shugaban gamayyar Kungiyoyin Ahlus-Sunnah na Afirka, Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau.
Shugabannin JIBWIS daga jihohin Najeriya, malamai, daraktoci da wakilan sassa daban-daban na Kungiyar sun halarci taron.
A yayin taron, Sheikh Bala Lau ya karɓi makullan wani sabon bangare na ginin Twins Theater daga hannun kamfanin da aka bai wa aikin, ta hannun Daraktan Ayyuka na Kungiyar. Ginin, wanda ya lakume fiye da naira miliyan 360, an yaba da ingancin aikin da aka kammala.
Har ila yau, shugaban ya karɓi rahotanni daga daraktocin sassa kan abubuwan da suka aiwatar da kuma shirin fara sababbin ayyuka. Ya kuma bukaci Kwamitin tattara fatun layya da su tsara tsarin karɓar sadakar fata cikin tsari da inganci, tare da kira ga al’umma da su tallafa da fatun layya.
Babban Sakataren Kungiyar, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, ya bayyana ci gaban da aka samu a aikin gina jami’ar, da gudunmawar kuɗi da mambobin Kungiyar ke bayarwa don ganin an kammala aikin.
Shugaban Majalisar Malamai, Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo, ya jaddada bukatar biyayya ga shugabanci da muhimmancin haɗin kai da taimakekeniya a tsakanin mambobin Kungiyar.
Muhimman batutuwan da aka tattauna sun haɗa da:
Ci gaban ginin jami’a
Ayyukan Kwamitin kula da marayu
Tsarin karɓar fatun layya
Taron ya gudana cikin kwanciyar hankali da fahimta, tare da ƙara ɗorewar haɗin kai a tsakanin shugabannin Kungiyar daga faɗin Najeriya.