Shettima Ya Kaddamar da Jirgin Farko na Aikin Hajji 2025 a Owerri.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09052025_201340_Screenshot_20250509-211254.jpg



Maryam Jamilu Gambo 

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya kaddamar da jirgin farko na aikin Hajjin bana 2025 daga filin jirgin sama na Owerri, jihar Imo, inda ya bukaci a gudanar da aikin cikin kwarewa, tsari, da kishin ƙasa.

Taron ya samu halartar gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma, shugaban NAHCON Farfesa Abdullahi Saleh Usman, da Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, tare da wasu jami’an gwamnati da shugabannin addinai da gargajiya.

Shettima ya jaddada cewa aikin Hajji ba wai tafiya tabdon ibada ba ce kawai, har da nauyin ƙasa da al’umma. Ya gargadi jami’ai da masu ba da hidima da su guji sakaci, tare da tunatar da maniyyata cewa su ne wakilan Najeriya a ƙasa mai tsarki.

Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana cewa adadin maniyyatan Hajjin bana ya kai 64,188, inda mutum 315 za su tashi a jirgin farko daga yankin kudu maso gabas—abin da ya nuna ci gaba a harkar hajji a Najeriya.

Gwamna Uzodimma ya bayyana tarihinsa da nasarorin da jihar ta samu, musamman wajen karɓar addinai daban-daban. Sarkin Musulmi ya yabawa gwamnan bisa kokarinsa na haɗin kai da goyon bayan ayyukan addini a jihar.

Tashin jirgin Air Peace daga Owerri ya nuna farkon aikin jigilar maniyyatan Hajji na 2025, wanda NAHCON ke shirin kammalawa cikin makonni biyu.

Follow Us