Makarantar Imam Abu Hanifah Ta Yaye Dalibai 13 Masu Haddar Alƙur’ani a Katsina

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimesA ranar Lahadi, 22 ga Yuni, 2025, makarantar Imam Abu Hanifah da ke Dutsin-Safe cikin garin....

Katsina City News June 23, 2025  ·  12:00 AM
| 1,151 Views
Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimes

A ranar Lahadi, 22 ga Yuni, 2025, makarantar Imam Abu Hanifah da ke Dutsin-Safe cikin garin Katsina ta gudanar da bikin yaye dalibai 13, maza da mata, waɗanda suka kammala haddar Alƙur’ani mai girma, ƙarƙashin jagorancin shugaban makarantar, Malam Murtala.

An gudanar da taron walimar cikin nishadi da girmamawa, inda ‘yan uwa, abokan arziki, malaman addini da shugabannin al’umma suka halarta. Daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron akwai wakilin Magajin Garin Katsina, Alhaji Aminu Abdulmumini Kabir, wanda Alhaji Abdu Ilyasu ya wakilta.

Daliban da aka yaye sun gabatar da bitar haddarsu a bainar jama’a, tare da nuna kwarewa da ƙwarewar da suka samu a harkar Alƙur’ani. A cikin jawabin sa, Alhaji Abdu Ilyasu ya yi bayani kan muhimmancin ilimi, yana mai ƙarfafa iyaye da su ci gaba da tallafawa ‘ya’yansu wajen samun ilimi mai nagarta.

Shugaban makarantar, Malam Murtala, ya yaba da hazaka da ɗa’a da daliban suka nuna, tare da kira ga sauran dalibai da su ƙara dagewa domin cimma burin da iyayensu suka sanya gaba.

Makarantar Imam Abu Hanifah na koyar da ilimin addini da na boko a lokaci guda, domin sauƙaƙa wa iyaye nauyin tarbiyya da kuma tallafawa gwamnati wajen bunƙasa ilimi da kyawawan ɗabi’u a tsakanin matasan jihar Katsina.

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 3 + 5?