Auwal Isah Musa | Katsina Times
Al'ummar unguwar Filin Folo Katsina a ranar Asabar din nan 5 ga Yulin 2025, sun shirya taron yi wa jihar da kasa baki daya addu'ar samun zaman lafiya da matsalar tsaro, tare da walimar murnar aikin hanyar da gwamnatin jihar za ta yi wa yankin nasu.
Taron addu'ar wanda ya gudana ne a Masallacin Juma'a na Filin Polo da ke Ramin Kura Ring-road, ya samu halartar dimbin al'ummar unguwar yara da manya.
Malam Ibrahim Iyal babban mataimakin kwamandan Hisba ta jihar, kuma babban limamanin Masallacin, a hudubar da ya gabatar a wajen, ya bayyana muhimmancin addu'a ga Musulmi, ya kuma kwadaitar game ds kyautatawa Musulmi ta kowace hanya, inda ya bayyana hanyar da za a yi wa yankin a matsayin daya daga kyautata wa al'ummar Musulmi daga gwamnan jihar, Malam Dikko Radda da yake shirin aiwatar al'ummar yankin.
Na'ibin Masallacin, Malam Kabir, shi ma ya yi huduba a taron, inda karfafi al'umma wajen taimakekeniya a tsakaninsu, hadin kai, da aikata duk abin da zai kusanta mutum ga mahalicci.
Wanda ya jagoranci shirya taron, dan gwagwarmaya Salmanu, ya bayyana taron addu'ar a matsayin na samun zaman lafiya ga jihar da karin kariya ta musamman ga gwamnan jihar Malam Dikko Radda, a daya bangare ya kuma bayyana walimar a matsayin ta murna ga aikin hanyar da za a soma aiwatar masu.
Salmanu, ya bayyana cewar al'ummar yankin sun shafe tsawon lokaci suna bi da neman gwamnatocin baya su yi masu wannan hanya wadda ta tashi daga kofar 'yandaka ta bi da Filin Polo, Ramin kura ta hade da Ring-road, amma ba a yi ba sai yanzu da gwamnatin Dikko Radda ta zo "ga shi zai share mana hawaye". In ji shi.
Da yake jawabi a taron addu'ar a matsayinsa na wakilin gwamnan jihar a taron, shugaban hukumar tsabtace muhalli na jihar Katsina (SEPA), Alhaji Muhammadu Kabir Usman Amoga ya bayyana taron addu'ar a matsayin abin da ya fi dacewa ga jihar daga al'ummar musamman halin da ake cikin na matsalar tsaro kodayake yanzu matsalar na saukaka sosai, sannan ya bayyana jama'ar yankin a matsayin masu kishin jihar da gwamnatin jihar.
Amoga, ya bayyana hanyar da za a yi masu a matsayin wadda za ta kawo wa yankin ci gaba kwarai da gaske, inda ya ce wannan na daga cikin kudurorin gwamnan jihar Malam Dikko Radda na kokarin bunkasa jin dadii da walwala ga katafanin al'ummar jihar.
A jawaban da daidaikun al'ummar unguwar suka gabatar a wajen, sun nuna jin dadi da farin cikinsu ga aikin hanyar, inda suka sha alwashin maida Biki ga gwamnan jihar a nan gaba.
A yayin addu'oi'n dai, an yi Saukar karatun Alkur'ani mai girma, addu'o'i da kuma hudubobi daga Malamai, sa'annan daga bisani aka rarra wa al'umma kudaden sadaka da kayan walima aka rufe da addu'a.