Rashin Gaskiya da Almubazzaranci: Bincike Ya Fallasa Bacewar Naira Miliyan 459 na Ayyukan Mazabu a Safana, Batsari da Danmusa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08072025_143855_Screenshot_20250708-153254.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

Duk da fitar da fiye da Naira miliyan 459 daga asusun gwamnatin tarayya don ayyukan mazabu a Safana, Batsari da Danmusa, a jihar Katsina. Yawancin ayyukan da aka ware kudin domin su ba su wanzu ba a zahiri. Wannan na cikin rahoton bincike na WikkiTimes tare da hadin gwiwar Shahararren mai barkwanci Dan Bello, inda suka gano cewa yawancin wadannan ayyuka ko dai ba a taba aiwatar da su ba ne ko kuma an yi su ne kawai a takardu.

A watan Janairu 2019, Hukumar FERMA ta fitar da Naira miliyan 12.2 don gyaran gadojin da ruwa ya rushe a Batsari. Bayan haka, ma’aikatar wutar lantarki ta biya Misterich Ltd Naira miliyan 67.8 don gyaran manyan gurbatattun hanyoyi a kan hanyar Katsina, Batsari, Safana, Karfi zuwa Funtua. Sai kuma a watan Fabrairu 2022, an sake biyan Allied Victory Nigeria Ltd Naira miliyan 39.3 don irin wannan aikin. Duk da haka, har yanzu titunan suna cikin halin lalacewa.

A shekarar 2022, kamfanonin Gorrion Engineering Ltd da Diamond Leeds Ltd sun karbi kudade har Naira miliyan 290 don sanya fitilun masu aiki da rana a kananan hukumomi ukun. Amma rahoton ya nuna cewa ko da fitilun da aka saka, ba su fi guda 30 ba a kowace Karamar Hukuma kuma da dama daga ciki ba sa aiki.

Wani mazaunin Danmusa, Aminu Lawal, ya bayyana cewa “Fitilun da aka saka sun fi karkata zuwa inda magoya bayan jam’iyyar ke zaune. Yanzu Danmusa har yanzu a duhu take.”

Puranova Nigeria Ltd ya karbi Naira miliyan 21.3 a 2019 don raba taki a Batsari. A 2024 kuma, wasu kudade sun sake fitowa daga cibiyoyin bincike da horar da manoma. Amma manoma da dama sun koka cewa ba su samu komai ba, sai magoya bayan jam’iyyar da ke mulki.

“A Safana, an raba buhu 80 ne kawai, kuma duk sun je hannun ‘yan siyasa,” in ji wani manomi, Yunusa Abdullahi.

A shekarar 2019, Prime Initiatives Consulting Ltd ya karbi Naira miliyan 22.8 don raba babura a LGAs hudu ciki harda Safana, Batsari da Danmusa. Amma binciken ya gano cewa babura 13 ne kacal suka isa ga jama’a gaba daya.

“Mun ga hotuna a Facebook, amma babu babur da ya shigo unguwarmu,” in ji wani mazaunin Safana.

Duk da kudaden da Misterich Ltd da Allied Victory Nigeria Ltd suka karba don gyaran hanya, mazauna Safana da Batsari sun bayyana cewa babu wani aiki da aka yi. A Safana, an ce an gyara wani kwalbati a Yantumaki, amma mazauna sun musanta hakan. Haka ma a Batsari, inda FERMA ta ce an gyara gadoji, amma babu alamar wani aiki.

Wasu ayyuka kuma kamar samar da na’urorin kwamfuta, samar da injinan lantarki da samar da wutar lantarki a kauyuka babu wani da ya tabbata. Kawai injin lantarki daya ne aka shigar a Bakin Kasuwa, Yantumaki, wanda ma baya aiki.

Rahoton ya gano cewa wasu daga cikin kamfanonin da aka ba kwangila kamar Gorrion Engineering da Diamond Leeds suna da shugabanni iri daya. Sauran kamfanonin kamar Puranova, Misterich da Thunder ICT Skills, ba su da shaidar gudanar da aiki a Katsina.

Mun nemi Hon. Iliyasu Abubakar, dan majalisa mai wakiltar yankin, domin jin ta bakinsa. Amma ya ki daukar waya, kuma ya ki amsa sakon da aka tura masa ta WhatsApp.

A Najeriya, ‘yan majalisa na amfani da matsayinsu wajen saka ayyukan mazabu cikin kasafin kudi, suna amfani da sunan cigaban al’umma. Amma su kan zabi kamfanonin da za su ba kwangila galibinsu kamfanonin da ba su da asali ko kuma na abokansu. Hakan yana ba su damar karkatar da kudade cikin sauki, ba tare da an hukunta su ba.
Wannan bincike na nuna irin yadda hanyoyin da suka kamata su kawo ci gaba ke zama wata hanya ta damfara da tauye ‘yancin jama’a. Yayin da akalla Naira miliyan 459 suka bace, al’umma na ci gaba da rayuwa cikin talauci, duhu da rashin ababen more rayuwa.

Follow Us