Daga: Muhammad Ali Hafizy. Katsina Times.

Kamfanin gidan man fetur na tarayyar Najeriya wato NNPC sun sake bude sabon gidan sayar da man fetur da kuma iskan gas akan farashi mai sauri a Katsina.
Taron kaddamar da gidan man ya gudana ne a ranar Talata 08 ga watan Yuli, 2025 a harabar gidan man dake bakin shataletalen "Liyafa Falace" bisa titin zuwa Dandagoro cikin birnin Katsina.
Manya daga cikin masu hannu da shuni a ma'aikatar NNPC ta kasa, sun samu halartar kaddamar da gidan man, tare da sauran yan kasuwa da kuma ma'aikatan bankuna, ya siyasa, al'umma maza da mata da sauransu.
Alhaji Umar Modi Yabo wanda yake shugaban hukumar NNPC ta jihar Katsina. Ya bayyana jin daɗin shi ganin yadda yan kasuwa da kuma al'umma suke bada gudummawar su wajen ganin an samar da gidajen mai mallakin gwamantin tarayya a jihar.
Modi ya kara da cewa. Samar da gidajen mai mallakin gwamantin tarayya, na daya daga cikin abubuwan da suke kawo ma jiha cigaba da kuma kasa baki domin ana saukakama mutane tare da sayar masu da mai mai inganci kuma cikin farashi mai sauki.
Hon. Yusuf Rabi'u Jirgede, wanda yake matsayin Kwamishinan ciniki na jihar, shi ne ya zama babban bako a wajen taron, kuma ya zama wakili ga gwamnan Dikko Radda a wajen taron.
A nashi jawabin ya yi jinjina ga ma'aikatar NNPC ta jihar Katsina da kuma ta kasa baki daya, aka irin cigaba da ake kawo wa jihar cikin yan kananan lokaci, y bayyana hakan a matsayin ci-gaba ga jihar da ma al'umma baki daya.