Gidauniyar Sardaunan Katsina ta shiga taron musayar ra'ayi kan inganta harkar Noma da ci gaban Kasa.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08072025_195253_FB_IMG_1752004305015.jpg

Auwal Isah Musa | Katsina Times 

Gidauniyar Sardaunan Katsina Ahmed Rufa'i Abubakar, ta shiga taron kasa kan "Ra'ayoyin Masana Game Da Inganta Amfanin Gona Da Hanyoyin Samar Da Su, Bunkasa su Don samun ingantaccen Abinci Da Dakile Talauci."

Taron na kwanaki biyu wanda aka fara gudanar da shi ranar Talata 8 ga Yuli, a birnin Katsina, inda za a kammala shi a ranar Laraba 9 ga Yuli, 2025 ya samu halartar Masana da masu ruwa da tsaki a fannin kimiyyar Noma da tattalin arziki.

Da yake jawabin a matsayinsa na maraba a taron, shugaban gidauniyar, Ambasada Ahmed Rufa'i Abubakar ya bayyana taron wanda gidauniyarsa ta shirya a matsayin na lalubo mafita wajen habaka harkan Noma don samun ingantaccen abinci ga al'ummar kasa, wanda a cewarsa ta wannan hanyoyin ne hatta Talauci zai ragu ga matasa da al'ummar kasar, inda ya bayyana Kamfanin 'Farm Katsina Limited' da aka kaddamar a jihar a ranar Litinin a jihar wanda ya kammalu a bisa tunaninsa da na wasu muhimman mutane, a matsayin misali, Kamfanin da zai inganta samar da albarkatun gona da sarrafa su, Itatuwa, da kuma abincin dabbobi.

"Yanzu haka (Kamfanin) yana sarrafa Madara da Nikakkiyar Masara har Ton 100, da kuma hada abincin dabbobi har na Ton 10." 

"Wannan wani karamin bangare ne daga gudummuwar da zamu bayar ga al'ummar kasa game da ta kwarewarmu don bunkasa harkar Noma a kasarmu." In ji shi

Dr. Umar Badaru Bindiri, Masanin a harkar Noma da zamanantar da su, shi ne wanda ya gabatar da Lakca a taron a matsayin Bakon ranar farko, ya bayyana yadda za a iya zamantar da kayyakin gona, har ma da wasu abubuwa da aka saba da su a tsarin gida zuwa tsarin 'Digital', wanda ya ce za kuma a fi saurin fahimta ko amfana da su fiye da tsohon tsarin da aka saba da su.

Dangane da Noman, Dr. Bindir ya bayyana cewar ya kamata mu san cewar Noma babban kasuwanci ne mai riba, kar a dubi matakan wahalar da ake sha kafin a kai ga cin moriyarsa.

Dr. Umar Bindir, ya hori al'ummar kasa musamman matasa da su yi kokarin saka jari a bangare Fasahar Noma da kirkire-kirkiren abubuwan ci gaba a cikinsa, yana mai bayyanawa karara cewar kuduri ko burin ci gaban harkar ba za ta zama mafita ga harkar ba muddin ba a tunanin da aiwatar da shi ba a zahirance.

"Sai da cikakke kuduri haduwa wajen aiwatar da shi za a iya juyar da dama zuwa arziki." Ya kwadaitar.

A jawabin rufe taron da ya gabatar, gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda, wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin jihar, Abdullahi Garba Faskari, ya nanata muhimmanci Noma ga ci gabanta jihar, inda ya bayyana shi a matsayin wani bangare da ya raya tattalin arzikin jihar da zamantakewar al'ummarta, yana mai cewar ya taimaka wajen dakile talauci a karkara da wadatar abinci.

Faskari, ya kuma bayyana gwamnatin jihar karkashin shugabanci Malam Dikko Radda a matsayin wadda ta saka manoma farin ciki bisa ga yadda ta samar masu kayayyakin Noma na zamani, yana mai bayyana cewar ta samar da na'urori, Taraktoci da sauran injunan noma don bunkasa Noma nasu.

"Jihar Katsina ta kuduri aniyar farfado da Noma ta hanyar amfani da Injinun noman rani da kuma inganta ababen more rayuwa."

"Ina mai bayyana maku cewar, gwamnatin jihar katsina na maraba da hadin gwaiwa da cibiyoyi irinsu gidauniyar Ahmed Rufa'i Abubakar domin cike gurabu da ake da gibinsu." - Ya karkare.

Masana a fannonin daban-daban a bangaren kirkire-kirkire da tattalin arzikin Noma, Jami'an gwamnati, shugabannin gargajiya, Malaman Makarantu, Wakilan cibiyoyi da shugabannin al'umma, 'yankasuwa da Manoma da sauran masu ruwa da tsaki a harkar ne suka halarci taron.

Ana sa ran a karshen taron za a samar da kyakkawan samakon don samun sauyi mai dorewa da zai inganta abinci daga albarkatun Noma wanda zai bunkasa tattalin arziki kasa, rage rashin aikin yi da kuma dakile fatara ga al'ummar kasa.

Follow Us