Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, Talata, 8 ga Yuli, 2025.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya bayyana muhimmancin rawar da kwararrun ma'aikatan kudi (Akawu) ke takawa wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin gwamnati. Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a ranar talata wajen taron Horo (Mandatory Continuing Professional Development – MCPD) na kungiyar "Association of National Accountants of Nigeria (ANAN) wanda aka gudanar a cibiyar taruka ta Continental Events and Sports Centre da ke Katsina.
Taron, wanda ya hada akasarin kwararru a fannin lissafin kudi daga sassa daban-daban na kasar nan, ya gudana ne bisa taken: “Haraji da Bin Ka’idoji: Dabarun Tabbatar da Ingancin Masu Lissafi a Sabon Zamanin Fasaha.”
A jawabin sa, Gwamna Radda ya bayyana cewa lissafin kudi ba kawai sana'a ba ce, illa dai ginshikin da ke dauke da adalci, gaskiya, da kuma ci gaban kasa mai dorewa.
“A matsayinku na masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziki, rawar da kuke takawa wajen inganta harkokin gwamnati ba za ta iya misaltuwa ba. Ku ne ginshikin gaskiya da rikon amana,” in ji Gwamnan.
Gwamnan ya kuma bayyana wasu muhimman matakan da gwamnatinsa ta dauka wajen yaki da cin hanci, ciki har da kafa Hukumar Yaki da Cin Hanci ta Jiha, Hukumar Dorewar Kudi, aiwatar da Asusun Bai Daya (TSA), da kuma shiga cikin shirin "Open Government Partnership" (OGP).
Shugabar ANAN ta kasa, Chief Hajiya Rakiya Talatu Kashimi, FCNA, ta yaba da irin goyon bayan da Gwamnatin Katsina ke bai wa kungiyar, tare da nuna gamsuwarta da yadda jihar ke tafiya a kan turbar gaskiya da ci gaba mai ma’ana.
“A karkashin jagorancin Gwamna Radda, an samu gagarumin ci gaba a bangaren tattalin arziki, tsaro, kiwon lafiya, ilimi da kuma fasahar zamani. Wannan jagoranci mai hangen nesa ne ke canza fasalin jihar Katsina,” in ji ta.
Shugabar ta bayyana cewa sauyin da ke faruwa a duniya na bukatar kwararrun ma’aikatan kudi su rungumi sabbin hanyoyin amfani da fasahar zamani kamar Artificial Intelligence da tsarin lissafi na zamani don kauce wa kura-kurai da inganta sahihancin haraji da bin doka.
Shugaban Kwamitin MCPD, Farfesa Hassan Ibrahim, ya bayyana cewa taron horon na shekara-shekara ana gudanar da shi ne a kowanne yanki na Najeriya domin kara ilimi da kwarewar ‘yan kungiyar ANAN. Ya ce taken bana na nuna yadda batun haraji ke zama abun mayar da hankali duba da sauye-sauyen da ke gudana a fannin kasafin kudi da dokokin hada-hadar gwamnati.
Shugaban ANAN reshen jihar Katsina, Shu’aibu Aliyu, ya bayyana godiya ga Gwamnan Katsina bisa daukar nauyin taron da kuma tallafawa kungiyar a fannoni da dama. Ya ce har yanzu babu wani nauyin da ke kan jihar a matsayinta na mai biyan dukkan kudaden horo na MCPD sama da shekaru ashirin.
“Gwamnatin Katsina na daya daga cikin wadanda suka fi nuna kishin bunkasa aikin lissafi da ma’aikatansa. An rika nada membobin ANAN a muhimman mukamai irin su Auditor-General na Jiha da kuma na Kananan Hukumomi,” in ji shi.
Wani bangare na taron ya hada da jawabi na musamman don girmama shugabar ANAN ta kasa ta 14, Chief Hajiya Rakiya Talatu Kashimi, inda aka yaba da irin nasarorin da aka cimma a karkashin jagorancinta. Haka kuma, an yi nuni da yadda jihar Katsina ke zama tamkar cibiyar tarihin Hausawa da al’adu da dama.
“Gwamna Radda ya bai wa wannan taro tagomashi ba kawai da halarta ba, har ma da kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya da ci gaban masana’antu da noma a fadin kananan hukumomi 34 na jihar,” in ji daya daga cikin mambobin Majalisar Gudanarwa ta ANAN.
Taron ya kammala cikin nasara, inda mahalarta suka bayyana gamsuwa da yadda aka tsara taron da kuma amfanin da suka samu a fannin haraji, doka da sabbin dabarun zamani.
HOTUNAN TARO: Da wakilan Katsina TIMES suka Dauko.
Gwamna Dikko Umar Radda yayin gabatar da jawabi a Taron MCPD na ANAN a Katsina. A tare da shi: Chief Hajiya Rakiya Talatu Kashimi (Shugabar ANAN),Dr Kayode Olushola Fasua, FCNA Chief Executive Officer, Prof. Hassan Ibrahim (Shugaban Kwamitin MCPD), da sauran manyan baki.