An rantsar da sabbin shugabannin hukumar gudanarwa ta Ilimin manya a jihar Katsina.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11072025_155207_FB_IMG_1752249054897.jpg



Auwal Isah Musa | Katsina Times 

Ma'akatar Ilimin Firamare Da Sakandare ta jihar Katsina a ranar Juma'a 11 ga Yulin 2025, ta gudanar da taron rantsar da sabbin shugabannin gudanarwa na Hukumar Ilimin Manya Ta Jihar Katsina (State Agency For Mass Education Board Members) a babban dakin taron Ma'aikatar.

Tun farko da farko da take gabatar da jawabi a matsayin mai jagorantar bikin rantsarwar, Kwamishinar Ma'aikatar Firamare Da Sakandare Ta Jihar, bayan ta taya sabbin shugabbanin murnar kasancewarsu a wannan mataki, ta fara da jinjina ga gwamnatin Malam Dikko Radda, bisa ga yadda ta ba wa bangaren Ilimi fifiko na musamman a fadin jihar, inda ta bayyana shugabannin da ake rantsawar a matsayin tabbacin haka, domin sai da aka yi tankade da rairaya kafin a zabo su a damka masu ragamar shugancin hukumar.

"Za6o ku a shugabancin wannan hukuma na zuwa ne bayan tabbatar da Inganci, jajircewa da kuma kwazonku a tarihin aikinku."

Daga nan, Hajiya Zainab Musawa ta hore su da su yi amfani da gogewarsu tare da zage damtse a yayin shugabancinsu wajen kawo gagarumin ci gaba da sauyi mai ma'ana ga Ilimi a fadin jihar, inda ta bayyana hakan a matsayin abin da ake da fatan gani daga gare su.

Bugu da kari, ta kuma hore su da su yi aiki da kishi gami da hadin kai a tsakanninsu, don a cimma nasarar da ake bukata.

"Ba zan yi tantamar cewar za ku hada kai da aiki tukuru a tare ba, wajen taimakawa junanku da shugabarku wacce za ku yi aiki tare da ita don a cimma nasara. Allah ya yi maku jagora a yayin gudanar da ayyukanku na shugabancin wannan hukuma." Ta karkare.

Ita ko a nata jawabin a wajen, Shugabar Hukumar Ilimin Manya Ta Jihar, Hajiya Bilkisu Kaikai,Ta bayyana yadda Ilimi ke samun gagrumin ci gaba a yanzu ta kowane fanni musamman a hukumar da take wa jagoranci, sakamakon ba wa bangaren dukkan abin da yake bukata daga gwamnan jihar Malam Dikko Umar Radda, inda ta bayyana gwamnan a matsayin 'shugaba mai hangen nesa'.

Hajiya Bilki Kaikai, ta kuma bayyana Kwamishina Hajiya Zainab Musan Musawa a matsayin wadda ta yi wa Ilimin jihar allurar wartsakewa nan-da-nan, sakamakon shugabancin Ma'aikatar da gwamna Radda ya mika mata jan ragamarsa.

A bikin rantsuwar, an bayyana Dr. Aisha Ladan a matsayin sabuwar Shugabar Hukumar Ilimin Baidaya Ta Jihar, a yayin da kuma Adamu Sule (Jibiya), Nazifi Abdulkadir (Batagarawa), Hajiya Saratu Ibrahim(Danja), da Sani Maibara (Baure) a matsayin masu taimaka mata wajen gudanar da shugabancin hukumar a bangarori daban-daban.

Wadandan suka halarci bikin rantsawar sun hada da: Shugabar din-din-din ta Ma'ikatar Ilimin Firamare Da Sakandare ta jihar, Hajiya Ummul-Khairi Bawa, Babban Sakataren Hukumar Kimiyya Da Fasaha ta jihar, Farfesa Kabir Ibrahim Matazu, da kuma Shugabar Hukumar Ilimin Manya ta jihar, Hajiya Bilkisu muhammad Kaikai, da sauransu.

Follow Us