Mu’azu Hassan, Katsina Times
A makon da ya gabata ne gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da bayar da hayar masaukin baki na Katsina Motel ga kamfanin OMU Resort Ltd, bisa yarjejeniyar zuba jari mai ƙima na Naira biliyan biyu da miliyan ɗari shida (₦2.6bn) a cikin shekaru goma.
Binciken da Katsina Times ya gudanar ya bayyana cewa kamfanin OMU Resort zai aiwatar da gyare-gyare da sabunta dukkanin sassan motel ɗin, gami da gina sabbin dakuna da sauya kayan more rayuwa. Haka kuma, daga cikin jarin da za a zuba, kamfanin zai biya gwamnati kuɗin haya na Naira miliyan 600 a tsawon shekaru goma, tare da biyan kuɗin shekara-shekara na Naira miliyan 60 ga gwamnatin jihar Katsina.
Bayan kammala wa’adin yarjejeniyar a shekara ta 2035, kamfanin zai dawo da mallakar motelin ga gwamnatin jihar Katsina.
Rahoton ya nuna cewa:
Idan aka cika duka sharuddan yarjejeniyar yadda ya kamata, hakan na iya haifar da gagarumin ci gaba ga tattalin arzikin jihar Katsina, musamman bangaren yawon bude ido da masaukin baki.
Binciken Katsina Times ya gano cewa OMU Resort Ltd kamfani ne da aka kafa a Jihar Lagos wanda ke gudanar da wuraren shakatawa da yawon bude ido a Asaba, Enugu, da Lagos. A halin yanzu ne kawai suka faɗaɗa ayyukansu zuwa jihar Katsina.
Kamfanin dai bai da babban tarihi a harkar gudanar da otel-otel, domin otel ɗinsu na farko “Le Chateau” an buɗe shi ne a 2021.
Duk da binciken da muka gudanar, ba a iya tabbatar da asalin kuɗin da OMU Resort zai zuba ba – ko bashi ne daga banki, ko tallafi ne daga haɗin gwiwa da wasu ‘yan kasuwa.
Wasu daga cikin mazauna jihar Katsina sun bayyana fargabar cewa sabon kamfanin kada ya kawo sabbin halaye ko ayyuka da zai ɓata tarbiyyar matasa, musamman idan aka buɗe wasu wuraren da ba su dace da al’adun al’ummar yankin ba.
Sun bayyana cewa suna fatan sabon kamfanin zai yi koyi da Hillside Royal Suites, otel da ke aiki cikin tsari da ladabi, tare da kafa gidauniya da ke taimaka wa al’umma. Hillside dai ya shahara da tsafta da mutunci a tsakanin otel-otel na jihar Katsina.
Ana sa ran sabuwar fuskar Katsina Motel za ta fara aiki a hukumance ranar 1 ga Oktoba 2025, a matsayin kashi na farko. Kashi na biyu kuma zai kammala a farkon shekarar 2026. A ziyarar da Katsina Times ta kai a wurin, an iske ayyuka na gudana cikin sauri da ƙwazo.
Katsina Times
www.katsinatimes.com
07043777779 | 08036342932