Katsina Times, – Laraba, 27 ga Agusta, 2025
Shugaban Karamar Hukumar Katsina Honorabul Isah Miqdad AD Saude ya sanar da fara shirin mako biyu na wayar da kan jama’a da tsaftace muhalli domin kawo ƙarshen yin bahaya a sarari a cikin garin Katsina.
A yayin taron manema labarai a ofishinsa da ke Shehu Musa Yar’adua House, kan titin Nagogo, Isah ya bayyana cewa za a gudanar da haɗin gwiwar wayar da kai, horarwa, da kuma aikin tsaftace muhalli a dukkanin yankuna 290 da ke ƙarƙashin hukumar.
“Burinmu shi ne kowane wurin da ake zubar da najasa a fili, dazuzzuka ko kasuwanni a tsaftace, a gyara, kuma a maido da su cikin yanayi mai tsafta,” in ji shi, yana mai jaddada cewa nasarar wannan aiki za ta sa hukumar ta cancanci samun takardar shaidar Open Defecation Free (ODF) daga UNICEF da sauran hukumomi.
Ya ce an tura ma’aikatan tsaftace muhalli fiye da 100 domin gudanar da aikin a dukkan unguwannin. Shugaban ya kuma amince cewa Karamar Hukumar Katsina tana daga cikin wuraren da matsalar yin bahaya a sarari ta fi yawa a jihar saboda yawan jama’a da kuma girman birnin.
Ya yi gargadin cewa yin bahaya a waje na janyo cututtuka masu haɗari irin su kwalara, typhoid da gudawa, tare da haddasa wa Najeriya asarar tattalin arziki da ya kai sama da kashi 1.3% na GDP a duk shekara.
Shugaban ya bayyana cewa shirin ODF ba wai tsaftace wuraren shara kawai ba ne, har ila yau yana nufin sauya halayen jama’a. “Ya na nufin kowane gida a gina ramin bayan gida, mutane su riƙa wanke hannuwansu da ruwa da sabulu, kuma tsafta ta zama ginshikin lafiyar jama’a,” in ji shi.
Ya roƙi shugabannin addini, sarakunan gargajiya, kungiyoyin farar hula da matasa su ba da goyon baya ta hanyar yada saƙon a cikin al’umma. “Muryar malamai daga masallatai da sarakuna ita ce mafi tasiri wajen sauya dabi’u,” ya ƙara da cewa.
Shugaban ya gode wa UNICEF, Babban Bankin Duniya, Hukumar Kare Muhalli ta Jihar Katsina da kuma Gwamnatin Jihar Katsina saboda tallafin da suka bayar wajen ci gaba da shirye-shiryen tsafta da samar da ruwan sha.
Ya jaddada cewa samun shaidar ODF ba ƙarshen tafiya ba ne, illa ma dai farkon hangen nesa na ganin Katsina ta zama ɗaya daga cikin kananan hukumomin da suka fi tsafta da lafiya a fadin ƙasar.
“Manufarmu ita ko wane gida ya samu bayan gida mai tsafta, kowace kasuwa da makaranta a riƙa tsaftacewa, kuma kowane yaro ya tashi a muhalli mai tsafta don kaucewa yaɗuwar cututtuka,” in ji shi, yana mai roƙon manema labarai su yada wannan saƙo a dukkan kafafen watsa labarai.