An Kama Wani Sojan Gona da Sunan Dan Majalisar Tarayya na Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes30102025_124137_FB_IMG_1761828038982.jpg


— Ya Yi Ikrarinsa da Cewa Yayi Ne Don Neman Ayyukan Yi Ga Matasan Katsina

Daga Katsina Times 

Jami’an tsaron farin kaya na Civil Defence Corps (NSCDC) sun kama wani mutum (mun ɓoye sunansa saboda dalilan tsaro) bisa zargin yin bogin cewa shi ne dan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta Tsakiya a majalisar tarayya.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron sun kama mutumin ne, bayan an same shi vda katin shaidar bogi da wasu takardu da ke nuna cewa shi ne dan majalisar tarayya.

An ce wanda ake zargin ya yi ƙoƙarin ganin shugaban hukumar farin kaya ne lokacin da jami’an suka gano cewa takardun nasa na karya ne.

Binciken jami’an tsaro ya kuma gano cewa sojan gonar ya taba samun ganawa da wasu jakadun ƙasashen waje, inda ya yi amfani da wannan matsayin na bogi wajen neman amincewarsu.

A cewar majiyarmu, wanda aka kama ya bayyana wa jami’an cewa ya dauki hayar mota ne tare da hadin kai da wasu mutane da ke taimaka masa wajen aiwatar da wannan danyen aiki.

Binciken Katsina Times ya gano cewa dan majalisar tarayya na gaskiya mai wakiltar Katsina ta Tsakiya, Hon. Sani Aliyu Danlami, ya je ofishin jami’an farin kaya domin sasanta batun, inda ya karɓi wanda ake zargin a beli, kuma yace a dakatar da shigar da kara a kotu.

A yayin hira da jaridar Katsina Times, wanda aka kama ya amsa laifinsa, yana mai cewa ya aikata hakan ne kawai don neman damar samar wa da matasan Katsina ayyukan yi.

Ya kara da cewa, “Kaddara ce ta kawo haka, ina rokon Allah Ya gafarta mini, kuma na yi alkawarin ba zan sake aikata irin wannan abu ba.”

Mutumin ya kuma gode wa Hon. Sani Aliyu Danlami bisa taimakon da ya yi masa wajen kubutar da shi daga tsauraran matakan doka.

Follow Us