Kungiyar Dikko Project Movement ta sanar a hukumance cewa ta amince tare da bayyana cikakken goyon bayanta ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da kuma Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, a babban zaɓen shekarar 2027.
A bisa wannan matsaya, kungiyar za ta kasance cikin sahun gaba tare da dukkan rassanta da mambobinta wajen haɗa kai da sauran ƙungiyoyi domin tabbatar da cewa Jam’iyyar APC ta samu nasara a kowane mataki na zaɓe mai zuwa, In shaa Allah.
Sanarwa daga:
Shugaban Kungiya,
Hon.Musa Yusuf Gafai
01/02/2026